
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gamayyar ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya (JOHESU) ta sanar da janye yajin aikin gama-gari da mambobinta suka shiga tun tsawon kwanaki 84 da suka gabata.
JOHESU ta ɗauki wannan mataki ne da nufin bai wa Gwamnatin Tarayya damar aiwatar da cikakken ababen da aka ƙulla yarjejeniya akan su tsakanin ɓangarorin biyu.
Hakan na zuwa ne bayan gudanar da wani zama na gaggawa da kwamitin zartarwar ƙungiyar ya jagoranta a Abuja, ranar Juma’a.
Tun a ranar 14 ga watan Nuwamba, 2025 ne JOHESU ta fara yajin aikin saboda rashin aiwatar da tsarin albashin da aka amince da shi ga mambobin nata daga ɓangaren gwamnatin tarayyar.
A wata sanarwa daga Shugabanta na Ƙasa, Kabiru Ado Minjibir da Sakatarenta, Kwamared Martin Adekunle Egbanubi, JOHESU ta ce kwamitin ya amince da dakatar da yajin aikin ne sakamakon shawarwari da jagororin ƙungiyar da kuma tattaunawa da wakilan gwamnati akan al’amarin.
A cewar sanarwar, dukkan ɓangarorin biyu sun amince da tsarin yarjejeniyar haɗaka ta CBA, wanda za a yi amfani da shi wajen warware matsalolin alƙawuran da aka gaza cikawa tun daga shekarar 2009 har zuwa yanzu.
