
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa na Musamman akan Harkokin Masarutu, Alhaji Abbas Tijjani Hashim, ya taya Hon. Nasir Bala Ja’oji kuma Adon Garin Ƙasar Hausa murna bisa naɗa shi a matsayin Daraktan Sabuwar tafiyar City Movement na Jihar Kano.
Tijjani Hashim ya bayyana hakan a matsayin abin da aka yi a lokacin da ya dace saboda kasancewar sa wanda yayi imani da ayyukan ci-gaban ƙasa da Shugaba Bola Tinubu ke yi kuma ya kasance babu dare ba rana cikin tallata Ajandar Sabunta Fata ta ‘Renewed Hope’, wadda ta ɗora Nijeriya a tafarkin dogaro da kai.
“Ina taya Adon Garin Kasar Hausa murna domin nadin ya sake tabbatar da gogewa da shugabanci da mika wuya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don ci-gaba da bunƙasar tattalin arziƙi da ɗorewar dimukraɗiyya”, inji shi.
A cewarsa, “sadaukarwa Ja’oji kan dimukraɗiyya da samar da shugabanci na gari sun tabbatar da cancantar ka na Shugaba da zai jagoranci wannan tafiyar domin sake samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu.”
Mataimakin Shugaban ƙasar na musamman ya ƙara da cewa, “ina imanin cewa City Movement a Jihar Kano za ta yi tasiri wajen tallata ayyukan cigaban Kasa ga Al’ummar Jihar Kano.”
A ƙarshe, ya yi masa addu’ar fatan alheri da samun nasara a tafiyar sake samun nasarar Shugaba Tinubu a karo na biyu.
