Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wannan kira na ƙunshe ne a wata ƙasida da hukumar ta gabatar a taron ƙungiyar ‘yan jarida reshen kafofin yaɗa labarai ta gudanar a Katsina.
Hukumar ta yi bayani kan illar rahoto da ya shafi tsaron ƙasa ba tare da tantance labarin ba.
Kan haka hukumar tsaron ta buƙaci haɗin kai tsakani jami’an tsaro da ‘yan jarida domin tabbatar da tsaron ƙasa.
Da yake buɗe taron, babban daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina Malam Maiwada Ɗanmalam ya bayyana wannan taron a matsayin abinda yake ya zo a kan gaɓa.
Ya yi fatan taron zai mai da hankali wajen gyara ɓarna da wasu ‘yan jarida masu amfani da yanar gizo da wani lokaci da suke yaɗa labarai na ƙarya da yana iya haddasa fitina a ƙasa.
Ya ce Gwamna Dikko Raɗɗa na yiwa taron fatan alheri tare da tabbatar da cigaba da bada goyon baya da haɗin kai ga manema labarai da gwamnatin sa domin cigaban jihar da ƙasa baki ɗaya wajen tabbatar da tsaro.
Shugaban ‘yan jarida reshen kafofin yaɗa labarai a Katsina Yusuf Ibrahim Jargaɓa ya bayyana cewa wannan taron ƙara wa juna sani ya zo akan mawuyacin halin na matsalar tsaro a ƙasar.
A wannan lokaci ake buƙatar manema labarai kan sanar da al’ummar halin da ake ce dangane da abinda ke faruwa kan abinda ya shafi tsaro wanda hakan ke jefa su cikin hatsari.
Kan haka shugaban ƙungiyar yayi kira ga ‘yan jarida da su riƙa sanya gaskiya da ƙwarewa a rahoton da suke gabatar wa.
Shima babban sakatare na ma’aikatan yaɗa labarai Malam Hassan Dan Ali wanda ya wakilci kwamishinan yaɗa labarai ya bayyana wannan taron ƙarawa juna sani da yace bai an ƙaru kawai kan harkokin tsaro ba har ma da ya shafi sauran al’ummar da shafi rayuwa.
Shugaban riƙo na ƙungiyar ‘yan jarida reshen jihar Katsina Kwamred Sama’ila Ahmad ya bayyana kasudu da hukumar DSS da Dr Sama’ila Balarabe ya gabatar ma matsayin masu inganci da zai taimaka wa mahalarta taron da sauran ‘yan jarida wajen tabbatar da rahoto mai sahihanci da ya shafi tsaron ƙasa.
