
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wasu da ake zargi mayaƙan Boko Haram/ISWAP ne, sun ƙwace wasu tireloli guda huɗu da ke maƙare da dabbobi, inda suka yi awon-gaba da sama da shanu 100 a kusa da Kareto da ke Ƙaramar Hukumar Mobbar a Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:25 na rana a ranar Litinin jim-kaɗan bayan manyan motocin sun bar yankin Damasak inda suka nufi Maiduguri, kamar yadda majiyoyin al’umma da na tsaro suka bayyana.
Al’amarin na kwanan nan ya faru ne ƙasa da kwana biyu da mayaƙan suak cinna wa wasu tirelolin wake guda huɗu wuta, waɗanda suke jigila daga Monguno zuwa Maiduguri a kusa da Garin Kashim na Ƙaramar Hukumar Guzamala, lamarin da ke nuna dawowar sabon al’amarin rashin tsaro a yankin arewacin Borno.
Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa mayaƙan sun tarw hanyar ne, inda suka ɗauki sa’a guda suna gudanar da atisayen jiran baki ɗaya tireloli huɗun su iso domin ƙaddamar da harin nasu.
Wata majiya ta ce, maharan sun fitar da dabbobin daga cikin motocin ne inda suka kuka kora su cikin daji.
Duk da wannan farmaki, direbobin tirelolin sun yi nasarar tserewa ba tare da wani abu ya same su ba.
Ɗaya daga cikin su ya ce al’amarin ya faru ne a ƙasa da mintina 30 da suka taso daga yankin Damasak, yana mai cewa mayaƙan suna samun damar ƙaddamar da hare-hare a yankin sakamakon rashin wadataccen jami’an tsaro babbar hanyar.
Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kula da hanyar Damasak zuwa Maiduguri kamar yadda ake yi wa yankin Gwoza, inda aka jibge dakarun tsaro domin bada kariya kowane hari da ka iya tasowa.
Mazauna yankin sun ce ire-iren hare-haren na haddasa koma-baya ga harkokin kasuwanci a yankin wanda yake ƙara zama da ƙara jefa al’umma cikin matsin tattali da suka jima aciki na tsawon shekaru sakamakon ayyukan tayar da ƙarar-baya.
