ADP ta caccaki Majalisar Dattawa kan sharuɗɗan miƙa sakamakon zaɓe ta na’ura

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar ‘Action Democratic Party’ ADP, ta bayyana damuwarta akan sabon gyaran dokar zaɓe da Majalisar Dattawa ta yi, wanda ya bada damar watsa sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura, saidai bai mayar da hakan wajibi ba.

Dokar ta kuma yi hukuncin yin amfani da takardar ‘Form EC8A’ a matsayin mafita matuƙar aka samu gazawar sadarwar intanet.

A wata sanarwa da ADP ta fitar ta hannun Shugabanta na Ƙasa, Injiniya Yabagi Yusuf Sani, jam’iyyar ta ce, duk da cewa janye matsayar farko da majalisar ta yi na ƙin amincewa da watsa sakamakon ta na’ura na nuna matsin lambar jama’a da kuma burin
dimukraɗiyya.

ADP ta jaddada cewa, duk wani gyara da bai tabbatar da watsa sakamako kai-tsaye kuma a zahiri ba, ba zai iya dawo da amincin zaɓe ba.

Watsa sakamako ta laturoni ba wani jin daɗin fasaha ba ne kawai, saidai ita ce babbar kariya daga maguɗin sakamako tsakanin rumfunan zaɓe da cibiyoyin tattara sakamako, wuraren da a tarihi ake samun manyan rikice-rikicen zaɓe a Nijeriya.

Ta ƙara da cewa mayar da tsarin watsa sakamako da aka saba bi a baya na nufin buɗe ƙofa ga rashin gaskiya da kuma shakku, wanda hakan ke cigaba da barin raunanan da ’yan Nijeriya cikin halin da ake nema fita daga cikinsa.

Har ila yau, Jam’iyyar ta yi gargadin cewa ba wa Form EC8A iko na doka idan aka ce an samu “gazawar intanet” na haifar da babbar barazana ta tsarin doka, wadda za ta iya:
“ƙarfafa uzurorin da ba za a iya tantance su ba, mayar da ikon yanke hukunci zuwa wuraren tattara sakamako marasa
bayyani, da kuma ƙara yawan ƙarar bayan zaɓe da za a iya kauce wa.”

A cewarta, “irin wannan sakamako bai dace da ruhin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) ba, wanda ya ɗora ikon ƙasa a hannun jama’a tare da wajabta gaskiya, riƙon amana, da kuma kawar da cin hanci a harkokin
gwamnati.”

Akan haka ne ADP ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta kammala wannan gyara ta hanyar kafa doka da za ta tanadi wajabcin watsa sakamakon zaɓe kai-tsaye ta lantarki daga kowace rumfar zaɓe.

By Babaji