Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata (3)

Spread the love

Daga AISHA ASAS

5. Shan ruwa isasshe a kullum:

Kamar yadda muka taɓa faɗa a wannan shafin shan ruwa ba wai iya kawar da ƙishi ne aikin sa ba kamar yadda mutane da dama suke gani. Muhimmancin ruwa yana da yawa a jikin ɗan adam, ciki kuwa har da fata. Domin fata na buƙatar ruwa don kasancewa cikin ƙoshin lafiya.

Isasshen ruwa a jiki na sanya fata ta kasance cikin damshi, wanda hakan ke hana ta bushewa da zai iya kai ga matsaloli masu yawa. Suna taimakon fata a ɓangaren laushi da kuma ƙyalin da ake buƙata. A taƙaicee ruwa na da rawar da suke taka wa a lafiyar fata da samun kyan ta.

6. Samun isasshen barci:

Barci dai kamar yadda muka sani wata ni’ima ce da Allah ya yi wa bayinsa da ke da matuƙar muhimmanci ga gangar jiki da ruhi na ɗan adam. A ɓangaren fata kuwa, rashin barci na ɗaya daga cikin ababen da ke sanya fata duhu, musamman dunhun zagayen ido, wanda ke hana fuska kyan gani, kuma rashin isasshen barci kan iya haifar da ƙuraje da wasu nau’ukan curutan fata da ba ma tunanin zai iya.

Kasancewar barci na awa 7 zuwa 9 ne fata ke buƙata don sabunta kanta, hakan na nufin matattar fata za ta fi sabuwa tasiri a jikin mai ƙarancin barci.

7. Rage damuwa:

A wani darasin da muka yi a shafin Kwalliya a baya, mun bayyana irin yadda damuwa ke tasiri ga lafiyar ɗan adam, saidai ba mu bayyana yadda take tasiri a fata ba. Damuwa na tsananta matsalolin fata kamar ƙuraje da eczema. Ma’ana waɗannan matsalolin fata da ma wasu kan yawaita ne idan akwai damuwa. Shi ya sa yin wasu daga hanyoyin kawar da damuwa kamar yin atisaye na daga cikin ababen da ake buƙata don kiyaye daidaiton fata.

By ukarofi