Watan Ramadan: Shin akwai gyaran gida a shirye-shiryen da ki ke wa azumi?

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Idan aka ce an zo irin wannan lokaci na kusa da azumi shire-shirye kan kankama daga wurin maza har mata, inda maza aljihunsu ne zai motsa yayin da mata ke shagalin shirya irin ababen da za a ci da sha har ma da fara shirin kayan sallah ga masu zurfin ido. Saidai abin tambayar mata nawa ne ke sanya tsaftar gidansu a cikin wannan shirin?

Mai karatu barka da kasance a cikin shafin Iyali na jaridar Blueprint Manhaja, sannunku da jimirin bibiyarmu. Ya shirye-shiryen azumi, Allah ya nuna mana shi lafiya ya datar damu.

A yau shafin namu zai yi tsokaci ne kan muhimmancin sanya gyaran gida a cikin tsarin shirye-shiryen da muke yi a cikin watan Ramadan, da kuma yadda mata da yawa ke kawar da kansu daga ba wa wannan ɓangaren muhimmancin da ya dace da shi.

Kasancewar watan azumi na da nauyi duba da irin yadda muke wuni da yunwa, wanda hakan kan gajiyar da mata da yawa, har ya hane su irin al’adar da suke da ita ta gyaran gida. Hakan ke sa a samu rauni a ɓangaren tsafta a cikin azumin.

Idan muka yi duba da yadda tsafta take cikin imani, ibada ma takan cika ne idan akwai tsafta, wannan zai fahimtar da mu cewa ta zama wajibi a cikin watan na azumi musamman ga masu yara ƙanana, duba da yiwar yin najasa a wuraren da za a iya yin sallah.

Akwai wani shiri da mata ke yi wa watan na azumi da yake da matuƙar kyau, duk da cewa ba addini ya ce ayi haka ba amma yana daga cikin al’adun da suke da kyau. Mata da yawa idan aka shigo satin ƙarshe na kama azumi, sukan yi gyaran gida da zai rage masu kaso mai yawa na tsafatar gidansu a cikin azumi.

Sukan yi amfani da ƙarfi wurin fitar da datti mai yawa daga gidansu, ta hanyar wanke manyan ababen kamar labule kujeru da kuma wanke kicin da sauransu. Hakan kan sawwaka masu tare da ɓoye rashin kuzarinsu a cikin watan azumi a ɓangaren tsaftace gida.

Allah ya gwada mana watan Ramadana lafiya, ya sa muna daga cikin bayin da za a ‘yanta alfarman manzon rahma S.A.W.

By ukarofi