DAGA JOHN D. WADA, a Keffi
Wata ƙungiya da ake kira masu goyon bayan sanata Wadada a ƙaramar hukumar Keffi jihar Nasarawa ta bayyana cikakken goyon bayan ta ga matakin gwamnan jihar Abdullahi Sule na tabbatar ya cika alƙawarin sa na mayar da ragamar mulkin jihar ga shiyar Yammacin jihar a zaɓen gwamnoni na shekarar 2027.
Ƙungiyar ta yi kira ga gwamna Abdullahi Sule ne a lokacin wani zagaye na goyon baya ga Gwamna Abdullahi Sule da shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Sanata Aliyu Ahmed Wadada da ke wakiltar mazaɓar yamma ta jihar a majalisar dattawa ta tarayya wadda aka shirya a fadar mai martaba Sarkin Keffi a garin Keffi ranar Laraba.
Da yake jawabi jim kaɗan kafin a fara gudanar da zagayen Darakta Janar na ƙungiyar Sanata Ahmed Aliyu Wadada, Lamaran Bello ya bayyana cewa ƙungiyar magoya bayan Sanata Wadada din sun yanke shawarar gudanar da zagayen ne don nuna amincewar su da salon shugabancin gwamna Abdullahi Sule da Bola Ahmed Tinubu tare da nuna goyon bayansu ga kokarin tabbatar da bai wa shiyar ta Yamma damar fito da ɗan takarar kujerar gwamnan jihar wanda zai gajeshi a inuwar jam’iyyar APC a shekarar 2027.
Yace bayan shiyar ta Yamma sun ɗauki sama da shekaru 20 suna jira har kujerar gwamnan ta zaga duka shiyoyin jihar yanzu lokaci yayi da yakamata a dawo da ita shiyar don tabbatar da adalci da riƙon amana.
D.G. Bello Lamaran ya ƙara da cewa har ila yau idan aka mai wa shiyar damar ƙungiyar tana kuma da amincin cewar Sanata Aliyu Wadada ne kaɗai cikin duka yan takaran zai iya ɗorawa daga inda gwamnan zai tsaya.
Daganan sai shugaban ƙungiyar Wadada ɗin Bello Lamaran ya kuma bayyana cewa sun kasance a fadar mai martaba Sarkin Keffin ne don samun albarkar basaraken kafin su fara gudanar da yaƙin neman zaɓe gadan gadan.
Shima da yake jawabi a madadin mai martaba Sarkin Keffi, wanda ya wakilceshi wato Alhaji Shamsudeen Maikasuwa wanda shine Fakacin Keffi ya yi fatan alheri ga ƙungiyar tare da bayyana goyon bayan masarautar ga wannan yunƙurin dawo da kujerar gwamnan jihar wa shiyar ta Yamma inda yace tabbas idan hakan ya faru aka kuma bai wa sanata Wadada damar zai cigaba da bunƙasa tattalin arzikin jihar da gudanar da shugabanci nagari kamar yadda yake yi a yanzu inda ya kuma buƙaci magoya bayan ɗan siyasan sun tabbatar sun gudanar da zagayen cikin kwanciyar hankali.
Yace a yanzu ma da Sanata Wadada bai hau kujerar ba yana cigaba da gudanar da ayyukan cigaba da ke kawo canje-canje masu ma’ana a rayuwar al’umma musamman yan karkara, sannan yace idan Wadada ya zama gwamnan jihar kowa zai more shi ne ba tare da nuna banbancin siyasa, addini ko ƙabilanci ba.
Wakilin mu ya rubuto cewa daga fadar Mai Martaba Sarkin Keffin ƙungiyar ƙarƙashin jagorancn D. G ɗin ta zaga lungu-lungu da sako-sakon ƙaramar hukumar inda ta nuna cikakken goyon bayan ta ga Gwamna Sule da kuma ubangidan su wato Sanata Aliyu Wadada inda daga bisani tawagar ta tsaya a babban ofishin kamfe na ɗan takaran gwamnan da ke nan G.R.A.
