
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da sunanan Ambasada Isma’il Abba Yusuf ga Majalisar Dattawa domin tantance shi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON).
Wannan naɗi wani ɓangare ne na Sashe na 3(2) na kundin dokar NAHCON na 2026, inda aka miƙa buƙatar hakan a hukumance ga majalisar a jiya Talata ta wata wasiƙa daga Fadar Shugaban Ƙasa.
A ciki Shugaba Tinubu ya nemi Shugaban majalisar,, Godswill Akpabio da ya jagoranci aikin tantancewa da tabbatar da Ambasada Abba Yusuf a muƙamin domin ba shi damar fara jagoranci ba tare da ɓata lokaci ba.
Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da tsohon shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yi murabus daga muƙamin, ƙasa da watanni 14 da naɗa shi.
Ambasada Yusuf jajirtaccen ɗan ƙasa da ne da ya samu ƙwarewa a harkokin difulomasiyya na tsawon shekaru da dama a gwamnati da harkokin ƙasa-da-ƙasa.
A ‘yan shekarun baya-bayan nan, ya yi aiki a matsayin jakadan Nijeriya ga Jamhuriyar Turkiyya daga shekarar 2021 zuwa 2024.
