NUJ ta buƙaci NEDC ta yi wa ’yan jarida inshora

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) ta buƙaci Hukumar Raya Arewa Maso Gabas (NEDC) da ta ɗauki nauyin biyan kuɗin inshorar lafiya ta ’yan jarida da ke aiki a yankin, domin kare rayukansu da lafiyarsu yayin aiki.

Shugaban NUJ na ƙasa, Alhassan Yahaya, ne ya bayyana hakan a lokacin da hukumar NEDC ta karɓi baƙuncin shugabancin NUJ na ƙasa da na Jihar Bauchi, tare da wakilan ’yan jarida daga Gombe, a ofishinta, domin tallafa wa ’yan jaridar da suka rasa kyamara da wayoyinsu sakamakon hatsarin mota da suka gamu da shi yayin aiki tare da hukumar a Jihar Bauchi.

Yahaya ya bayyana cewa NUJ ta ƙaddamar da tsarin inshorar haɗin gwiwa ga ’yan jarida, inda ake biyan kimanin Naira dubu 40 ga kowane ɗan jarida domin kare lafiyarsa da aikinsa daga haɗurra.

Ya ƙara da cewa, NUJ za ta ci gaba da yin haɗin gwiwa da NEDC domin tallata ayyuka da shirye-shiryen da hukumar ke aiwatarwa a yankin Arewa Maso Gabas.

By ukarofi