Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Tsohon Ministan Tsaro, Alhaji Lawan ɓatagarawa ya yaba da taron da ƙungiyar Masu Sayar da Abincin Buhu na Arewa “Grain Marketers Association of Northern Nigeria” reshen jihar Kano, suka gudanar a gidan Mumbayya don tattauna matsalolin ƙasa, inda ya ce ya kamata mutane su yi koyi da irin wannan mataki domin taimakawa ci gaban ƙasa.
Ya bayyana cewa ba kamar yadda mutane suka ɗauka cewa yan siyasa su ne su kaɗai za su iya warware komai ba, dole sai an haɗa kai da kowane ɓangare na al’umma. In aka sami cikakken haɗin kai sannan ne za a sami mafita mai ɗorewa.
Ya ce, al’amarin tsaro yana da tushe, idan babu kula da tushe na yau da gobe sai abu ya riƙa rikicewa. Tattaunawa inda kowa ya zo da irin nashi fahimta babu abin da ya fi shi muhimmanci. Su hukumomi a kowane mataki su ne ke da babban haƙƙi, amma duk ɗan adam na da haƙƙin bai wa hukuma goyon baya, duba da cewa yanzu a halin da ake ciki hukuma ta gaza kan harkar tsaro a ƙasar nan.
“In aka dubi yadda cikin yan kwanakin nan ɗimbin mutane da aka kashe a jihohin Kwara, Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kebbi da Neja, irin wannan kisan gillar ya zama kullum sai ka ji an je an rufe ƙauye an keta mutuncin maza da mata a gaban ya’yansu da jikoki. Babu wanda yake da haƙƙin bada cikakken tsaro sai hukumomi, amma kuma sun gaza,” cewar Lawan ɓatagarawa.
Ya ce matakin inganta tsaro ya ƙunshi a hana riƙe makamai daga wanda doka ba ta amince masa ba, a karɓe kuma duk wani sulhu da ake cewa ana yi da masu riƙe da makami ba bisa doka ba magana ce ta banza, domin ta yaya za a yi sulhu da wanda yake da makami ba a karɓe ba da wanda bashi da ko kokara, ace kuma wai an yi sulhu, sai dai ace an miƙa musu kai kawai.
Don haka tsohon ministan tsaron kuma manomi ɗan siyasa, Alhaji Lawan ɓatagarawa ya ce dole ne a ɗauki matakai da za su inganta tsaro sannan a duba yadda yawan mutane ke haɓaka a yi tsarin tattalin arzikin ƙasar nan. Yadda jama’a ke ƙaruwa kullum ya zamana tattalin arziƙi yana ƙaruwa, yadda mutane za su sami sana’oi da ayyuka da kasuwancin yi da za su ɗauki nauyin kansu da iyalinsu da dogara akansu, domin babban hatsari shi ne wanda bai ci abinci ba, ba maganar zaman lafiya da tsaro a wajensa. Don haka inganta tsarin tattalin arziƙi da kowa zai amfana zai taimaka wa kawar da matsalar tsaro.
A nasa ɓangaren, Alhaji Umar Abba Mustapha Ungogo, shugaban ƙungiyar masu samar da abincin buhu na Arewacin Nijeriya reshen jihar Kano ya bayyana maƙasudin taron don haɓaka tattalin arziƙi da zaburar da matasa ne, duba da irin halin da ake ciki a Arewa, inda abubuwa sun taɓarɓare sun kwaɓe, tattalin arziƙi da makomar matasa na cikin wani yanayi ga barazanar tsaro.
Ya ce sun lura a Arewa yawanci mutane na dogara da abu biyu da ake jira su yi aiki kuma a ɗora musu laifi. Mun tsaya barci muna zargin yan siyasa da yan boko da gazawa. Lokaci ya yi da za a daina zargin wasu, kowa ya tashi ya zage ya bada gudummuwa a ɓangarensa don kawo gyara. Don haka a ɓangarensu suka ga wace gudummuwa za su bayar da rawar da za su iya takawa kan sha’anin makomar cigaban goben Arewa.
Ya ƙara da cewa ana ganin irin abubuwan da ke faruwa, rashin aiki ya jawo matasa na shiga shan miyagun ƙwayoyi da aikata abubuwa da ba su dace ba. Da ace an kafa kamfanoni suna aiki, za a samawa ɗinbin matasa aiki a ciki, da irin abubuwan da ake ji na faruwa marasa kyau ba su faru ba.
Ya ce, taron ya shafi kowa ne, masana, malamai, yan siyasa da yan kasuwa da sauran al’umma. Don haka ya yi kira ga gwamnatoci a kowane mataki a ƙasar nan da cewa su yi duba da yadda Allah ya kawo sauƙin tsadar abinci, a ɗauki mataki na bayar da gudummuwa ga manoma domin a sami sauƙin tsadar taki da irin noma. Saukowar kayan abinci ya sa manoma ba su ci riba ba saboda noma da suka yi da tsadar kayayyakin noman.
Alhaji Umar Abba Mustapha Ungogo ya jaddada buƙatar gwamnati ta ɗauki mataki don sauko da taki da sauran kayan noma don rage wa manoma raɗaɗin da suke a ciki, su je su yi noman kayan abinci a damina mai zuwa. Domin in ba su yi noma ba saboda tsadar taki, ana hasashen tsadar kayan abinci da zai biyo baya sai ya fi na baya ma. Suna fata Allah ya kiyaye aukuwar hakan.
Hajiya Sayyida Sani Rogo, ɗaya daga cikin mata yar kasuwa yar siyasa, shugabar makarantar Islamiyya ta Idirisiyya dake Hotoron Arewa da ta halarci taron, ta bayyana jin daɗin halartar taron domin muhimmancin yan kasuwar buhu wajen bada gudummuwa a harkar abinci.
Taron dai ya sami halartar mutane da dama da suka haɗa da shugaban ƙungiyar masu sayar da abinci a buhu na Arewa, Alhaji Mustapha Sudawa, da sauran yan kasuwa daga ciki da wajen Kano da shehinan malamai na jami’a da na addini. Dakta Dukawa na daga waɗanda suka gabatar da jawabi a taron. Cikin mutane da suka bada tallafi a yayin taron sun haɗa da Alhaji Muhammad Adakawa, Hajiya Sayyida Sani Rogo, Alhaji Lawan Mai Masara da sauran mutane da dama.
