Nijeriya na buƙatar ci gaban kashi 10 duk shekara don kai wa tattalin arzikin Dala tiriliyan ɗaya – Ministar Kuɗi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Karamar Ministar Kuɗi, Dakta Doris Uzoka-Anite, ta bayyana cewa Nijeriya za ta buƙaci ɗorewar ci gaban tattalin arziki na aƙalla kashi 10 cikin 100 duk shekara a cikin shekaru goma masu zuwa domin cimma burin zama ƙasa mai tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya.

Ta bayyana hakan ne yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta ƙasa (NEC) da aka gudanar a Abuja a ranakun 9 zuwa 10 ga Fabrairu, inda ta ce duk da cewa tattalin arzikin ƙasar na nuna alamun farfaɗowa da kashi 4 cikin 100 a shekarar 2025, hakan bai isa ba wajen cimma babban burin sauyi mai zurfi.

A cewarta, ci gaban kashi 6 zuwa 7 cikin 100 na iya taimakawa wajen rage talauci, amma ana buƙatar ci gaba mai lamba biyu domin samar da sauyin tattalin arziki mai ɗorewa.

Ministar ta jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ta sauya salo daga kasancewa babbar mai kashe kuɗi zuwa mai buɗe ƙofa ga zuba jari, ta hanyar Tsarin Hanzarta Ci Gaban Cikin Gida (DGAS) da aka shigar cikin Shirin Ci Gaban ƙasa na 2026–2030.

Ta bayyana cewa sabon tsarin ya gabatar da abin da ta kira “Kasafin Zuba Jari”, wanda zai rage haɗarin zuba jari, tare da jawo jarin masu zaman kansu har sau uku zuwa biyar fiye da kuɗin da gwamnati ta ware.

“Dole ne rawar da gwamnati ke takawa ta sauya daga zama babbar mai kashe kuɗi zuwa mai sauƙaƙa zuba jari da buɗe hanyoyin jawo jarin masu zaman kansu. Gwamnati kaɗai ba za ta iya ɗaukar nauyin sauyin da muke nema ba,” inji ta.

Dangane da hasashen kasafin kuɗin 2026, Uzoka-Anite ta ce ana sa ran samun kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 34, tare da ƙaruwar rabon haraji zuwa GDP zuwa kusan kashi 18 cikin 100, sakamakon aiwatar da Sabuwar Dokar Haraji ta 2025 da kuma daidaita tsarin haraji a jihohi.

Ta kuma bayyana cewa Babban Bankin Nijeriya na da burin sauƙaƙa hauhawar farashi zuwa ƙasa da kashi 13 cikin 100 kafin ƙarshen shekara, bisa la’akari da sake inganta jarin bankuna, samun rarar cinikayya da kuma ajiyar kuɗaɗen waje da suka haura dala biliyan 40.

Ministar ta yi nuni da cewa bisa yadda ake ware kuɗaɗe a halin yanzu, zai dauki sama da shekaru 111 kafin a tara dala biliyan 300 da ake buƙata domin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa, sai dai idan an rungumi tsarin da zai haɗa jarin gwamnati da na masu zaman kansu.

Ta kuma gargaɗi cewa sauyin farashin mai a kasuwar duniya, tangardar samar da abinci da matsalolin sauyin yanayi na iya kawo cikas ga burin ci gaba, tare da kira ga haɗin kai tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi domin tabbatar da cewa daidaiton tattalin arziki ya fassaru zuwa ingantaccen rayuwa ga ‘yan ƙasa.

By ukarofi