Dubban jama’a sun fito zaɓen raba gardama a Bangladesh

Spread the love

Dubban jama’a sun fito zaɓen raba gardama a Bangladesh, a zaɓen da ake kallon sa a matsayin makomar sabuwar siyasa bayan kifar da tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina a 2024 sakamakon bore na matasa (Gen Z).

Mutane kusan miliyan 128 ne ke da rajistar kaɗa ƙuri’a, kuma zuwa rana ta tsaka, kaso 32.88% sun riga sun kaɗa ƙuri’unsu a yawancin cibiyoyin zaɓe 42,651.

Zaɓen na fuskantar hamayya tsakanin kawancen jam’iyyun BNP ƙarƙashin Tariƙue Rahman da kuma Jamaat-e-Islami ƙarƙashin Shafiƙur Rahman. Hasashen ra’ayin jama’a na nuna BNP na da rinjaye.

A birnin Dhaka, masu kaɗa ƙuri’a sun fara taruwa tun kafin buɗe rumfunan zaɓe da ƙarfe 7:30 na safe. Wasu sun ce wannan ne karo na farko cikin shekaru 17 da suka ji cewa ƙuri’arsu na da muhimmanci.

Wani mai kaɗa ƙuri’a ya ce: “Yana kama da ranar Idi. Mutane sun cika da farin ciki da ƙwarin gwiwa.”

An jibge jami’an tsaro kusan 958,000 daga ‘yan sanda, sojoji da jami’an paramilitary a faɗin ƙasar. Duk da cewa ba a samu rikici mai tsanani ba, an ruwaito mutuwar wani jigo na BNP a wata arangama, da kuma fashewar ƙaramin bam a yankin Gopalganj.

A lokaci guda, ana gudanar da ƙuri’ar raba gardama kan sauye-sauyen kundin tsarin mulki, ciki har da kafa gwamnatin riƙon ƙwarya mai zaman kanta a lokutan zaɓe, ƙara yawan wakilcin mata, da ƙayyade wa’adin Firaminista zuwa sau biyu kacal.

Masu sharhi na ganin cewa idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya kuma kowa ya amince da sakamakon, hakan zai zama babbar shaida cewa Bangladesh ta fara sabon babin dimokuradiyya.

By ukarofi