Faransa ta miƙa batun jami’in diflomasiyya mai alaƙa da Epstein ga masu shari’a 

Spread the love

Gwamnatin Faransa ta sanar da masu gabatar da kara kan wani jami’in diflomasiyya mai suna Fabrice Aidan, wanda ake zargi da aikewa Jeffrey Epstein da wasu takardu na Majalisar ɗinkin Duniya.

Sunan nasa ya bayyana a fiye da takardu 200 da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta fitar.

Ministan harkokin wajen Faransa ya bayyana zargin a matsayin “mai matuƙar muni,” inda aka fara binciken cikin gida da kuma matakan ladabtarwa.

Ana zargin ya tura sakonnin imel daga asusun sa na ƙashin kansa da kuma na Majalisar ɗinkin Duniya tsakanin 2010 da 2016.

Wata majiya ta kusa da Shugaba Emmanuel Macron ta ce, ya yi matuƙar takaici da abin da ya fito fili. Ana sa ran masu gabatar da ƙara za su yanke shawarar ko za a buɗe binciken laifin.

Lamarin ya sake jawo hankalin duniya kan sabbin fayilolin Epstein da ke bankaɗo alaƙar manyan ‘yan siyasa da masu faɗa a ji a Turai da Amurka.

By ukarofi