Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na wannan mako, sannunku da jimirin bibiyar jarida mai farin jini, Blueprint Manhaja.
A wannan makon, za mu tattauna kan darasin da a wannan zamani ya fi ci wa mata tuwo a ƙwarya tsayin lokaci, musamman ma a ƙasar Hausa.
kafin mukai ga tattauna ƙorafin mata kan rashin ciyar da su da mazansu ke yi, bari mu fara kan mazan wanda wataƙila mu samo wata mafita ko fahimta a cikin lamarin.
Akwai wani lokaci can bayan a kafar sadarwa ta ɗ wanda a baya aka fi sani da Twitter da wani bawan Allah ya wallafa cewa, wani lokacin ya kan ji tamkar ya gudu ya bar iyalinsa saboda kawai yana jin sun zame masa kaya. Abin mamaki, bai kasance talaka ba, duk da cewa shi ba mai kuɗi ne sosai ba, amma yana da abinda zai iya kula da iyalin daidai misali.
A lokacin sai na faɗa dogon nazari kan me zai sa magidanci irin wannan tunani, shin saboda matsala da yake da ita da matar ko ‘ya’yan? Ko ba ya samun yadda yake so a wurin matar? Ko kuwa rashin so ne na uwar ya shafi ‘ya’yan? Da sauran tambayoyi.
Saidai a irin sharhin da aka yi wa rubutun nasa sai na samu amsar cewa, duka tambayoyin da na yi wa kaina ba su da alaƙa da zancen nasa, domin maza da yawa sun bayyana cewa, su ma sukan ji hakan a wasu lokuta, kuma ba wai don ba sa son matansu ba, ko don sun yi masu wani laifi ko rashin abin basu ba.
A iya fahimtar da na yi daga kalaman magidantan waɗanda suna da yawa, sai na fahimci cewa, wani abu ne na ajizanci na ɗan adam, wato gajiyawa ne wanda yake zuwa ga mutumin da ya jima yana abu ɗaya, wanda za mu iya kira da ruwan dare a zukatan mazan aure. Saidai waɗanda suke bari abin ya yi tasiri a aikace ne za a kira mutanen banza ko waɗanda ba su kyauta ba.
Misali idan ka ɗauki zancen namiji ya ga wata mace a waje ta birge shi, wannan ɗabi’a ce da aka sani ga maza sananna, wadda duk da ban san sahihancin hadisin ba, na taɓa jin wani malami ya kawo shi, a lokacin da yake karantarwa kan ayar da ta yi magana kan aure da yadda yake zama hanyar nutsuwa da kare kai ga mazaje, inda ya ce, ” Wata rana Manzon Allah (S.A.W) yana zaune tare da sahabbai Allah ya ƙara yadda da su, (sai wanda ya ruwaito hadisin, wanda na manta sunan da faɗa) ya ce, sai wata mata ta wuce ta gabanmu, sai manzon Rahma ya miƙe ya shiga gida, bayan ɗan lokaci ya fito. Sai mukaga ruwa suna saukowa daga gashin kansa, alamar ya yi wanka.”
Idan wannnan hadisin ya kasance mai isnadi mai kyau, za mu iya fahimtar cewa, Annabin Rahma na koyar da su cewa, matanku hanya ce ta kawar da kai daga faɗawa alfasha. Hakan na nufin za ka iya ganin mace ta ba ka sha’awa, amma mafi alheri su ne waɗanda za su kawar da kai su koma zuwa ga iyalansu don biyan buƙata ta halastaciyyar hanya.
Anan kenan ɗabi’a ce gare su, saidai waɗanda suka fi ƙarfin zuciyarsu ne mafifita. Haka na fahimci wannan lamari na son tserewa ɗawainiyar iyali.
Kamar yadda wani ya faɗa, “lokuta da dama na kan ji ina ma zan iya barin gari, na nisanta da iyalina, ya kasance ba na tunanin kowa sai kaina, babu mai jiran in ba shi, babu wanda ya zame min dole na damu da shi. Amma sai na yi saurin tunatar da kaina, waɗannan da ka tara fa bisa zaɓi ka tara su, kai ka samarwa kanka asalin samuwarsu ta hanyar auran uwarsu, ka sanar da iyayenta ka shirya ɗauke nauyinta daga kansu zuwa kanka. Da ka kawo ta ita kaɗai aka ba ka, kai ne dai ka yanke shawarar ka kai kuma ka shirya ƙara yawansu daga biyu zuwa har ko nawa kuke a gidan. Ba wani wurin ta je ta ɗauko su ba, kuma ba wani ya kawo su ya tursasa ka ba. Kuma su yaran ba su san kowa ba fa sai kai a ɓangaren ɗawainiya, sun zama kai, kai ma ka zama su, don haka duk inda ka je, dole ka dawo, domin rayuwarka ba ta taɓa cika sai da su a ciki.” Ya ce da waɗannan kalaman ne nake farkar da zuciyata daga wannan mafarki.
Da yake ba wannan ne darsain namu gaba ɗaya ba, don haka ba za mu zurfafa ba sosai, saidai zuwa nan mun samu abinda muke son yin gini a kansa, wato dai akwai gajiyawa da ɗawainiyar iyali a zukatan magidanta, wanda masu hankali daga cikinsu ke bar wa zuciyarsu.
Wannan ɗabi’a ko tunani na wasu mazan kan yi tasiri a zamantakewarsu da iyalansu, wanda ba wai dole sai sun gudu ba, a’a wasu na iya ɗauke hannunsu daga wasu ɗawainiyar iyalinsu, har akai lokacin da shaiɗan zai yi tasirin da zai sa su ɗauke hannun gaba ɗaya.
Ciyarwa na ɗaya daga cikin manya-manyan ginshiƙan aure, wanda har Musulunci ya bayyana su a ƙarƙashin ababen da za a iya raba aure don rashin su. Da wannan ne za mu iya cewa, rashi ne kawai zai iya zama hujjar da za a iya kallo a matsayin yin haƙuri da yanayin. Amma idan mun ɗauki ciyarwa za mu iya cewa shi ne ginshiƙi na biyu a layin haƙoƙin aure.
Za mu ci gaba.
