
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanata Barinada Mpigi da ke wakiltar santoriyar Ribas ta Kudu maso Gabas a Majalisar Dattawan Nijeriya ya rasu.
Sanatan ya shefe kimanin sama da shekaru goma yana aiki a Majalisar Dokoki ta Ƙasa, sannan ya rasu yana da shekaru 64 a duniya.
A ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026 ne marigayin ya rasu a wani asibitin Landon bayan fama da wani gajeren rashin lafiya.
Haka kuma ana kallon sa a matsayin na hannun daman Ministan Abuja Nyesom Wike.
An haife shi ne a ranar 23 ga watan Yunin 1961.
An fara zaɓen Mpigi a Majalisar Wakilai a shekarar 2011, inda aka sake zaɓar sa a karo na biyu a shekarar 2016. A shekarar 2019 kuma aka zaɓen shi a matsayin Sanata a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Kazalika, shi ne Shugaban Kwamitin Haɗin-gwiwa na Majalisar Dattawa da aka kafa domin binciken satar ɗanyen mai a yankin Neja-Delta.
Tuni dai Gwamna Siminalayi Fubara ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da makusantan marigayin kamar yadda Sakataren watsa labaransa, Onwuka Nzeshi ya bayyana a wata sanarwa.
