Da dama sun rasu a harin mayaƙan Lakurawa a ƙauyukan Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mutane da dama ne suka rasu bayan mayaƙan Lakurawa sun ƙaddamar da hare-hare a wasu ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Arewa da ke Jihar Kebbi a ranar Laraba.

A cewar majiyoyin al’umma da na tsaro, maharan sun je yankunan ne da ke gundumar iyaka inda suka yi ta harbe-harbe acikin jama’a.

Wasu alƙaluma da majiyoyin tsaron suka fitar sun bayyana cewa aƙalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu a yankin Mamunu, biyar a Awashaka, uku a Masama da kuma biyu-biyu a sauran ƙauyuka biyar da al’amarin ya shafa.

Wannan farmaki ya jefa al’ummar ƙaramar hukumar cikin firgici, inda da dama daga cikinsu suka bar gidajensu domin samun mafaka a wasu wurare kasancewar har gida maharan ke shiga suna harbe su.

Tuni dai aka baza jami’an tsaro a yankin domin ƙarfafa tsaro ga ƙauyukan, taimaka wa waɗanda suka tsira da kuma ƙoƙarin daƙile hanyoyin da maharan ka iya bi wajen tserewa.

Da yake tabbatar aukuwar al’amarin, Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar, Bashir Usman ya ce za a fitar da ƙarin bayani a kai da zara an kammala bincike.

By Babaji