Yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi haƙƙi ne na kowa da kowa – NDLEA

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano 

Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), reshen Jihar Kano, Dahiru Lawan Yahaya, ya bayyana cewa yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da safarar su haƙƙi ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa, duba da yadda matsalar ke ƙara addabar al’umma.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a da ta gabata yayin ganawarsa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Kano. A cewarsa, duk da irin ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen dakile matsalar, ba za a samu cikakkiyar nasara ba sai da haɗin kan al’umma ta hanyar bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri kan masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, maboyarsu da kuma masu safararsu.

Kwamandan ya ce hukumar na goyon bayan dokar da Masarautar Kano ta fito da ita ta yin gwajin miyagun ƙwayoyi ga masu neman sarauta, yana mai cewa matakin ya taimaka matuƙa wajen rage yawan masu amfani da ƙwayoyi. Ya ƙara da cewa ba masu neman sarauta kaɗai abin ya shafa ba, har ma da ɗaliban da ke neman shiga manyan makarantu da masu neman aiki.

A cewarsa, wannan tsari wani shiri ne da Shugaban NDLEA na ƙasa, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya assasa, inda Masarautar Kano ta ɗauke shi tare da mai da shi doka. Ya ce manufar gwajin ita ce gano waɗanda ke fara amfani da ƙwayoyi domin a taimaka musu tun da wuri, ba wai don hukunta su ba.

Dahiru Lawan ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa goyon baya da tallafin da take bai wa hukumar domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata. Haka zalika ya yaba wa shugabannin ƙananan hukumomi bisa samar da ofisoshin NDLEA a yankunansu, yana mai cewa hakan zai ƙara kusantar da ayyukan hukumar ga al’umma.

Ya yi kira ga iyaye da su riƙa sanya ido kan ‘ya’yansu, su san abokan hulɗarsu da wuraren da suke zuwa, tare da kira ga mazauna unguwanni da kada su bari yankunansu su zama mafakar masu shaye-shaye. Ya jaddada cewa matsalar shaye-shaye barazana ce ga zaman lafiyar al’umma, don haka dole ne kowa ya taka rawarsa.

By ukarofi