
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Darakta Janar na Hukumar Wayar da kan Al’umma ta Ƙasa (NOA), Mista Lanre Issa-Onilu ya yi kira ga ‘yan jarida da su dawo da tsari na daidai da ruwaito sahihan labarai domin masalahar ‘yan Nijeriya.
Issa-Onilu ya bayyana haka ne a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin Ƙungiyar ‘Yan jaridar Binciken Ƙwaf (NGIJ) ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Abdulrahman Aliagan a ofishinsa, ranar Juma’a.
Ya bayyana aikin jaridar binciken ƙwaf a matsayin wani ginshiƙi na ƙara wayar kan al’umma da ci-gaban dimukraɗiyya ta yadda hakan zai kasance madogara na wayar da kan al’umma.
Ya kuma jaddada cewa aikin jaridar yana taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da ƙasa gaba ta hanyar bayyana adalci, daidaito da ƙin fifita wani ɓangare.
Daraktan ya kuma koka akan abin da ya kira da yawan dakatar da aikin jaridar binciken ƙwaf a Nijeriya, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen haddasa koma-baya ga aikin jarida da yawaitar yaɗa labarai masu ruɗarwa da rarraba kan jama’a.
A cewarsa, aikin jarida na cigaba da samun tangarɗa bisa yadda aka bijire wa fassara ko abin da haƙiƙanin hujjojin ruwaito labarai suka ƙunsa.

