Ramadan: NULGE a Katsina ta yi kira ga Musulmai da su taimaka wa mabuƙata

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 

Shugaban ƙungiyar Ma’aikatan ƙananan Hukumomi reshen jihar Katsina, Kwamred Nasiru Wada Mai’adua ya yi wannan kira a wata takardar sanar wa da aka rabawa manema labarai.

Ya ce a wannan wata ma daraja ya zama wajibi masu hali su fito su tallafawa Marayu, Masu buƙatar na musamman da marasa ƙarfi.

“Ya zama wajibi mu fito mu tallafa wa waɗannan mabuƙata da kayan abinci,kuɗi da sutura domin suma su sami natsuwa wajan gudanar azumin watan Ramadan”,inji shugaban NULGE.

Kwamared Wada Mai’adua ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa da yan majalisu na kasa da shugaban kananan hukumomi da sauran manyan jami’an gwamnati da suka fara raba tallafi na kudi da kayan masarufi ga al’ummar sabanin azumi.

Ya yi kira ga masu hali a jihar da su bi sahun wadannan shugabanni wajan raba irin wannan tallafi da yace Allah zai mai da masu da abinda ya fi haka.

Haka kuma ya jawo hankalin wasu yan kasuwa da ke kara farashin kayan masarufi da sauran kayan bukata a wannan wata mai tsarki da su tsohon Allah su dai na.

Shugaban ƙungiyar ya danganta bala’o’in da ke addabar yankin da  halayen irin waɗannan yan kasuwa.

Kwamared Nasiru Wada ya kuma jajantawa yan kasuwan Kano kan iftala’in gobara da shafa da fatan Allah mai da masu da abinda yafi haka

By ukarofi