Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
An yi kira ga mawadata da ‘yan kasuwa da su ƙara ƙaimi wajen tallafa wa marasa ƙarfi da mabukata a wannan wata mai alfarma na Ramadan.
Babban Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kano Shawara kan Harkokin Kasuwannin Abubakar Rimi, Singa da Galadima, Hon. Musbahu Abdullahi Shado, ne ya yi wannan kira yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinsa.
Ya ja hankalin ‘yan kasuwa da su sassauta farashin kayayyaki, musamman waɗanda aka fi amfani da su a lokacin azumi, domin bai wa al’umma damar gudanar da ibada cikin sauƙi. A cewarsa, Ramadan wata ne na tausayi da taimakon juna, don haka ya kamata masu hali su tallafa wa marasa ƙarfi domin samun lada da rahamar Ubangiji.
Hon. Shado ya kuma jajanta wa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a makon da ya gabata, wadda ta haddasa asarar dukiya mai tarin yawa. Ya yi addu’ar Allah Ya mayar musu da abin da suka rasa tare da kare aukuwar irin haka nan gaba.
Haka kuma ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa ziyarar da ya kai kasuwannin domin ganin irin asarar da aka yi da idonsa, tare da bayar da tallafin naira miliyan ɗari ga waɗanda abin ya shafa.
Mashawarcin ya kuma yaba da ayyukan raya kasuwanni da gwamnatin jihar ke aiwatarwa, musamman gina tituna masu fitilun hasken rana da magudanan ruwa, yana mai cewa waɗannan ayyuka za su inganta zirga-zirga da tsaro tare da bunƙasa harkokin kasuwanci.
A ƙarshe, ya yi kira ga ‘yan kasuwa da sauran al’umma da su ci gaba da bai wa gwamnatin jihar goyon baya da haɗin kai tare da addu’o’i domin samun nasarar ayyukan ci gaba da za su taimaka wajen haɓaka tattalin arzikin Kano.
