Hukumar PHIMA da KHETFUND sun gudanar da taron bita ga masu maganin gargajiya a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

A ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kano na inganta harkokin lafiya a matakin farko, Hukumar Kula da Cibiyoyin Lafiya Masu Zaman Kansu ta Jihar Kano (PHIMA) tare da haɗin gwiwar KHETFUND sun shirya taron bita na yini guda ga shugabannin masu maganin gargajiya daga ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kano, Farfesa Salisu Ahmad, ya bayyana a yayin taron cewa Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, na ƙoƙarin ganin an inganta tsarin kula da lafiya musamman a matakin farko, la’akari da cewa masu maganin gargajiya na daga cikin waɗanda al’umma ke fara tuntuɓa idan aka samu rashin lafiya.

Farfesa Salisu ya ce manufar taron ita ce wayar da kan masu maganin gargajiya kan yadda za su kare kansu daga cututtuka masu yaɗuwa, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakaninsu da likitocin zamani domin rage yawaitar cututtuka a cikin al’umma. Ya ƙara da cewa akwai shirye-shiryen ci gaba da horas da su a duk tsawon shekarar nan domin bunƙasa iliminsu da inganta ayyukansu.

A cewarsa, cututtuka masu yaɗuwa na iya watsuwa ta hanyoyi daban-daban, ciki har da numfashi, don haka ya zama wajibi a ba su ilimin kariya domin su kare kansu da ma marasa lafiyar da ke zuwa wajensu. Ya jaddada cewa masu maganin gargajiya sukan fara hulɗa da marasa lafiya kafin su kai ga asibitoci, saboda haka ya zama dole su san lokacin da ya kamata su tura mara lafiya asibiti domin yin gwaje-gwaje.

Farfesa Salisu Ahmad ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da aka koya musu, tare da yaɗa shi ga sauran abokan aikinsu domin a samu sauyi mai ma’ana wajen dakile cututtuka masu yaɗuwa a jihar.

A nata jawabin, Shugabar Riƙo ta PHIMA kuma Daraktar Mulki, Hajiya Khadija Hussain Sa’id, ta bayyana cewa taron bitar ya zama dole ne ganin yadda ake samun ɓullar cututtuka masu yaɗuwa a cikin al’umma, kuma galibi masu maganin gargajiya ne matakin farko da ake zuwa.

Ta bayyana cewa wasu cututtuka na iya kama da mura ko tari, amma daga baya a gano wata cuta ce mai hatsari kamar mashako ko wasu cututtuka masu saurin yaɗuwa. Ta ce rashin sani kan irin waɗannan cututtuka na iya jefa rayuwar mai bayar da magani cikin haɗari.

Hajiya Khadija ta jaddada muhimmancin amfani da kayan kariya kamar takunkumi da safar hannu kafin taɓa mara lafiya, tana mai cewa dole ne mai ba da magani ya fara kare kansa kafin ya taimaki wani. Ta kuma yi nuni da cewa ba duk cuta ba ce za a iya gane ta ba tare da gwaji ba, don haka akwai buƙatar tura marasa lafiya asibitoci idan alamar cutar ta fi ƙarfin abin da za su iya magancewa.

Ta ƙara da cewa jihar Kano na da cibiyar kula da cututtuka masu yaɗuwa tare da ofisoshi a kowace ƙaramar hukuma. Mahalarta taron daga ƙananan hukumomi 44 za a ba su lambobin gaggawa domin su riƙa sanar da hukumomi idan sun gano wani lamari da ka iya zama barazana ga lafiyar jama’a.

Hajiya Khadija Hussain Sa’id ta bayyana jin daɗinta bisa yadda masu maganin gargajiya da sarakunansu suka amsa gayyatar taron mai taken “Wayar da Kai kan Cututtuka Masu Yaɗuwa a Cikin Al’umma.” Ta ce gwamnatin jihar ce ta bai wa PHIMA damar shirya taron tare da haɗin gwiwar KHETFUND domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin masu maganin gargajiya da likitocin zamani.

A ƙarshe, ta ce idan aka samu cikakken haɗin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, za a samar da al’umma mai ƙoshin lafiya tare da rage yaɗuwar cututtuka a fadin jihar Kano.

By ukarofi