Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Kungiyar Fulani ta Kautal Polako reshen Jihar Kano ta bayyana cewa Fulani mutane ne masu zaman lafiya, ilimi da sana’o’i, kuma ba su da alaƙa da ayyukan ta’addanci kamar yadda ake zargin wasu daga cikinsu.
Shugabannin ƙungiyar sun bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano, inda suka yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kiran da ya yi musu domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi rayuwarsu.
Shugaban shiyyar Kudancin Kano, Abdullahi Auta, ya ce taron ya nuna kulawa da girmamawa da gwamnati ke bai wa Fulani, yana mai jaddada cewa za su ci gaba da zama masu biyayya ga doka da zaman lafiya.
Hajiya Hauwa Abdu Zanasabe, shugabar mata ta shiyyar Kudancin Kano, ta ce Fulani na taka rawar gani a fannoni da dama na cigaban Arewa da Nijeriya baki ɗaya. Ta kuma roƙi gwamnati ta cika musu alkawuran da ta ɗauka, ciki har da samar da ruga-ruga da kasuwar nono.
