Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shalkwatar Tsaron Nijeriya (DHƙ) ta tabbatar da zuwan sojojin Amurka su 100 yankin Arewa maso gabas.
A cikin jawabin da ya fitar a ranar Litinin da yamma, Samaila Uba, mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya, ya ce, sojojin Amurka sun sauka a jihar Bauchi tare da kayan aikinsu.
An a sa ran rundunar sojin Amurka za ta bai wa sojojin Nijeriya horaswa, sai dai ba ba za su shiga filin daga ba kamar yadda mahukuntan ƙasashen biyu suka bayyana.
“Dakarun dai sun iso Nijeriya ne domin yin aiki da sojojin Nijeriya,” in ji Uba.
“Ya ce zuwan dakarun abu ne da aka tsara shi biyo bayan roƙon gwamnatin Amurka da ta turo dakarunta Nijeriya da nufin horas da jami’an sojinta da tallafa musu wajen musayar bayanan sirri.”
Kakakin rundunar sojin ya ce, haɗin guiwar zai ƙarfafa dakarun Nijeriya ta hanyar samun horaswa da zai taimaka musu wajen yaƙi da ‘yan ta’adda a fadin ƙasar nan.
Ya kuma ce dukkan horaswar za a yi ne a ƙarƙashin kulawar gwamnatin Nijeriya tare da haɗin kan rundunar sojin Nijeriya.
“Rundunar sojin Nijeriya a shirye suke wajen ƙara inganta ayyukansu domin yaƙi da ‘yan ta’adda da ke barazana ga ƙasar nan ta fuskar tsaro da kuma walwalar al’umma,” ya faɗa, inda ya ƙara da cewa shalkwatar tsaron Nijeriya na “bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin yin komai a buɗe ba tare da kuskure ba kuma fitar da bayanai game da haɗin guiwarta da sojojin Amurka a kan lokaci.”
Manhaja ta rawaito daga New York Times cewa sojojin Amurka su 100 ne isa Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Jaridar ta ce jirgin farko na sojojin Amurka ya sauka ne a ranar Alhamis. Ta ce sojoji guda 100 ne jirgin ke ɗauke da su.
Izuwa ranar Juma’a da yamma, wasu ƙarin jiragen Amurka sun sauka a Nijeriya tare da kayan aikinsu.
Jaridar Manhaja ta rawaito cewa dakarun Amurka za su tallafawa wata ƙaramar tawagar sojoji da ta fara sauka a Nijeriya.
Dakarun sojojin na zuwa ne bayan watanni da matsin lambar shugaba Trump wanda ya soki gwamnatin Nijeriya kan abin da ya kira da gazawa wajen kare Kiristoci daga fuskantar hare-hare da wasu ƙungiyoyi ‘yan ta’adda ke kai musu.
Gwamnatin Nijeriya tare da sauran masu sa ido a cikin gida sun ce wannan hare-hare ba iya Kiristoci ya shafa ba har da Musulmai.
A ƙarshen, shugaba Trump ya ba da umarni harba rokoki ta sama a ranar Kirsimeti da sunan kai wa ‘yan ta’adda hari a yankin Arewa maso yamma da ake zargi da kashe Kiristoci.
Da yawan ‘yan Nijeriya sun nuna damuwarsu game da tura dakarun sojojin Amurka kan shiga harkokin cikin gida la’akari da irin yadda hakan ya haifar da matsala a wasu ƙasashe da suka shiga a baya.
Sai dai a cikin jawabin da kakakin rundunar sojin Nijeriya ya fitar, Uba ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa haɗin guiwar tasu za ta mutunta ‘yancin ‘yan Nijeriya.
Sai dai Uba bai yi ƙarin haske kan na tsawon wanne lokaci ne dakarun sojin Amurkan za su shafe ba a Nijeriya.
