Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki domin samar da wadata da ci gaba mai ɗorewa ga ’yan Nijeriya kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
A wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Adamawa, Tinubu ya bayyana cewa sauye-sauyen da ake aiwatarwa na fara haifar da sakamako a fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya da ababen more rayuwa.
Ya yaba wa gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri, kan yadda yake amfani da kuɗaɗen rabon tarayya wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa, musamman a ɓangaren hanyoyi da ilimi.
Shugaban ya buƙaci gwamnatocin jihohi su ƙara zuba jari wajen rage talauci da inganta ilimi, tare da gode wa shugabannin gargajiya da na addini kan rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai.
A nasa jawabin, Fintiri ya gode wa shugaban ƙasa bisa ziyarar da ya kai jihar da kuma ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka, tare da tabbatar masa da cikakken goyon bayan jihar.
