Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Mukaddashin Hakimin Gundumar Darmanawa a Masarautar Tarauni, Alhaji Salisu Abdullahi Na’ibawa, ya jajanta wa ‘yan kasuwar da gobara ta shafa a makonnin da suka gabata, ciki har da kasuwar ‘yan katako ta Kurna, da kasuwannin Singa da Galadima a Jihar Kano.
Basaraken ya miƙa saƙon jajen ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kasuwar ‘Yan Katako Na’ibawa, inda ya bayyana lamarin a matsayin babbar asara da ta girgiza al’umma.
Ya nuna tausayinsa ga waɗanda lamarin ya shafa, tare da kira gare su da su rungumi ƙaddara da haƙuri, yana mai cewa duk wata jarabawa daga Allah tana tare da lada ga masu juriya.
Alhaji Salisu ya kuma yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa, domin ko da ba za a iya mayar da abin da suka rasa ba, tallafi zai taimaka wajen rage radadin asarar da suka yi.
Haka zalika, ya ja hankalin al’umma da su ƙara dagewa wajen yin addu’o’i da neman taimakon Allah domin samun sauƙi daga irin waɗannan iftila’o’i.
A ƙarshe, ya roƙi ‘yan kasuwa da su sassauta farashin kayayyaki musamman a wannan lokaci na ibada, domin al’umma su samu sauƙin gudanar da rayuwarsu tare da neman rahamar Allah.
