Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Abdullahi Ghali Basaf, ya bayyana cewa babban burinsa tun kafin hawansa mulki shi ne tallafa wa al’umma musamman a ɓangaren ilimi, wanda ya bayyana a matsayin ginshiƙin rayuwar ɗan Adam da tushen duk wani ci gaba da ɗaukaka.
Hon. Ghali Basaf ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai a lokacin da yake ƙaddamar da rabon takardun shaidar ɗaukar nauyin ɗalibai 900 ‘yan asalin ƙaramar hukumar domin yin karatun NCE a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi. An gudanar da taron ne a ɗakin taro na Rabiu Musa Kwankwaso da ke harabar kwalejin a ranar Lahadi da ta gabata.
Ya ce tun bayan zuwansu mulki, harkar ilimi ce ta fi samun fifiko a manufofinsu, inda a baya suka ɗauki nauyin ɗalibai 1,100 tare da tura wasu 100 zuwa makarantun koyon harkokin lafiya. Ya ƙara da cewa sabon shirin ɗaukar nauyin ɗalibai 900 zai taimaka wajen cike gibin ƙarancin malamai a makarantun ƙaramar hukumar tare da gina al’umma mai ilimi da dogaro da kai.
Shugaban ya kuma jaddada cewa shirin tallafin karatun ba zai tsaya nan ba, domin za su ci gaba da tallafa wa matasa domin su samu damar ilimi mai inganci. Ya shawarci ɗaliban da su zama jakadun ƙaramar hukumar nagari yayin karatunsu, tare da maida hankali domin cin gajiyar damar da aka ba su.
Hakimin Kumbotso, Barden Kano Alhaji Abdullahi Nabila Sunusi, ya nuna farin cikinsa tare da yaba wa shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan ƙoƙari na tallafa wa marasa hali domin su samu ilimi. Ya bayyana cewa al’umma mai ilimi tana samun ci gaba ta kowanne fanni, tare da fatan ɗaliban za su bayar da sakamako mai kyau domin fitar da shugaban kunya.
A nasa jawabin, Dr. Danyaro Ali Yakasai ya bayyana ilimi a matsayin ginshiƙin rayuwar ɗan Adam, yana mai cewa abin yabawa ne yadda shugaban ƙaramar hukumar ke ƙoƙarin samar wa matasa abin dogaro da kansu ta hanyar ɗaukar nauyin karatunsu.
Shugaban ɗaliban Basaf Gida Gida, Zailani Bala Kura, ya tabbatar da cewa ɗaliban za su maida hankali kan karatunsu domin su cika burin da aka sa a gaba. Ya ce ba abin mamaki ba ne yadda shugaban ya fifita ilimi, la’akari da irin ɗimbin ɗaliban da ya ɗauki nauyinsu tun bayan hawansa mulki.
