Ramadan: Gwamnan Gombe ya buƙaci Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya buƙaci Musulmi da dukkanin mazauna jihar su yi amfani da watan Ramadan wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban Najeriya.

A saƙon taya murnar fara azumi, gwamnan ya ce Ramadan lokaci ne na ibada, gyaran hali da kusantar da kai ga Allah.

Ya roƙi al’umma su yi addu’a kan ƙalubalen tsaro da matsalolin tattalin arziƙi da ƙasar ke fuskanta.

Ya bayyana cewa azumi ba hana abinci da shan ruwa kawai ba ne, yana kuma koyar da adalci, tausayi da aikata gaskiya.

Ya ƙara da cewa lokaci ne da ya dace a yi addu’a domin shugabanni su samu nasara wajen jagoranci.

Gwamnan ya kuma buƙaci malamai da limamai su yi amfani da wa’azi wajen ƙarfafa zaman lafiya da fahimtar juna, tare da guje wa saƙonnin da za su haddasa rarrabuwar kai.

Haka kuma, ya roƙi masu hali su taimaka wa marasa galihu a watan, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba da inganta rayuwar al’umma.

A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya bai wa Musulmi yin ibada karɓaɓɓiya a watan Ramadan.

By ukarofi