Zaɓen Abuja: Jami’an EFCC sun je rumfunan zaɓe a Lugbe don hana rabon kuɗi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyun siyasa da dama suna yunƙurin raba wa masu zaɓe kuɗaɗe domin saye ƙuri’unsu a rumfunan zaɓe da ke yankin Lugbe a Birnin Tarayya Abuja.

An gano cewa akwai wasu wakilan jam’iyyar ADC da na wasu jam’iyyu suna bai wa masu zaɓe kuɗaɗe, kamar yadda Blueprint.ng ta ruwaito.

Wannan al’amari ya sa jami’an Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, suka garzaya wajen domin binciken waɗanda suke da hannu aciki.

Saidai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu bayani kama koda mutum guda, saidai an ga yadda wasu ɓata-gari ke ƙoƙarin tayar da fitina a wajen zaɓe da ƙoƙarin korar jama’a.

Masu fafutukar gaskiyar zaɓe sun buƙaci a hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan aiki, tare da ƙarfafa tsaro da sa ido a sauran rumfunan zaɓe domin hana faruwar dukkan abin da ka iya kawo cikas.

By Babaji