Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Kungiyar Majalisar Sasanta Matsalolin Ma’aikata ta ƙasa (JNC), reshen jihar Kano, da haɗin gwiwa da ofishin shugaban ma’aikata na jihar Kano, ta shirya bitar kwana biyu ga ma’aikata da suka kusa yin ritaya domin koya musu hanyoyin sana’o’i da za su iya dogaro da kansu bayan sun bar aiki.
Shugaban ƙungiyar Majalisar Sasanta Matsalolin Ma’aikata ta ƙasa, reshen jihar Kano, Kwamared Hashim A. Saleh, ya ce a shekarar 2024 suka nemi gwamnatin jihar Kano ta ba su taimakon kuɗi ta ƙarƙashin ofishin ma’aikata. Suka haɗa kai da masana da suka bar aiki da waɗanda suke ciki, suka koyi ilimi, sannan suka ga dacewar abin da suka koya su zo jihar Kano su taimaki duk wanda zai ritaya a wannan shekarar ta hanyar ba shi horo don ya ƙarfafa shi tun yana aiki.
Ya ce duk da za a iya cewa an makara, amma ba haka ba ne, domin cikin wata uku ko huɗu za a ba ka ilimin da za ka fara tunani kafin ka gama aiki. ɗan ilimin da ka samu zai sa ka fara ɗan ƙirƙirar wasu abubuwa. Suka ga ya kamata su zo su faɗaɗa shi a jihar Kano, kuma ba tare da sun nemi taimakon kuɗi daga gwamnatin jiha ba. Sun tattara kuɗaɗe a tsakanin ƙungiyoyin da suke da su suka shirya taron na kwana biyu.
Kwamared Hashim A. Saleh ya ce mahalarta taron 500 ne za a ba su horo da shaida a fannin noma ko harkar lafiya ko ta sadarwar zamani. Bayan sun yi wannan, za su kai su ƙananan masana’antu su nuna musu yadda abubuwa suke a aikace, a zahiri. Ba don komai ba, ba sa so su ga mutum ya bar aiki ya wayi gari bai san inda zai dosa ba, wannan ne dalilin shirya taron.
Ya ce suna neman a nan gaba su faɗaɗa taron, gwamnati ta shigo ciki, kuma sun gamsu da irin abubuwan da Gwamnatin Kano take wa ma’aikata, da suka haɗa da ɗaukar ƙarin ma’aikata a kowane ɓangare, biyan albashi akan kari, ƙarin girma akan lokaci da kyautata duk abin da ya shafi ma’aikata.
Ya ƙara da cewa suna neman a duba batun bashin da ake bayarwa ga ma’aikata daga N300,000, a duba abin da ya cancanta daidai da yadda za a iya sayen mota, domin a wannan lokaci abin da ake bayarwa na bashin sayen mota bai isa ko babur a saya ba. Sannan a duba yawan ƙarin albashi da ake yi duk shekara da dokar ƙasa ta tanada.
Kwamared Hashim A. Saleh ya ƙara da roƙon Gwamnan jihar Kano ya tallafa musu da za su haɗu da ƙungiyoyin ma’aikata gaba ɗaya su gina fili da za su riƙa ayyuka a ciki, maimakon su riƙa neman wajen da za su riƙa irin wannan horo. Su zuba kayayyakin da za a riƙa bayar da horo, hakan zai sauƙaƙa wa duk ma’aikaci, ko ya bar aiki ko yana ciki, ya riƙa zuwa yana yin horo na koyon sana’o’i daban-daban.
Ya kuma roƙi Gwamnatin Kano ta tallafa wa ƙungiyar tasu da mota domin sauƙaƙa musu tafiye-tafiye. Suna roƙon gwamna ya sahale a ba su mota, domin duk inda suka je da ita za a ga alamar Gwamnatin Kano ce ta bayar, hakan zai ƙara mata mutunci da kima kan yadda take kulawa da ma’aikata.
Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban ƙungiyar Kwadago ta ƙasa, wanda shi ne Shugaban ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya ta ƙasa, Kwamared Kabiru Ado Minjibir. Ya nuna farin ciki da jin daɗi da shirya bitar don koyawa waɗanda za su yi ritaya a wannan shekara sana’o’i da suka ƙunshi ilimi, harkar lafiya, noma, kafofin sadarwa na zamani da kasuwanci.
Ya yi nuni da cewa wannan abu ne mai kyau, ya kamata a ce an ɗabbaƙa shi ya zama ma abu na matakin ƙasa, domin duk ma’aikacin da ya soma aiki ya san wata rana zai bari, ko in ya cika shekarunsa na aiki ko na haihuwa.
Ya yi kira ga ƙungiyoyin da suke kula da ma’aikata da su ci gaba da fito da irin wannan tsari. A ƙungiyarsu ta ƙasa ta ma’aikatan lafiya da yake shugabanta, ya yi alƙawarin ɗaukaka tsarin zuwa shugabancin ta na ƙasa domin kai shi dukkan jihohin Najeriya, ma’aikatan lafiya su amfana.
