El-Rufa’i ya shigar da ƙarar biliyan N1 akan ICPC kan kai samame gidansa na Abuja

Spread the love

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El‑Rufai, ya kai ƙara a kotu na neman a biya shi tara Naira biliyan 1 saboda abin da ya kira mamaye gidansa ba bisa ka’ida ba da jami’an Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka (ICPC) suka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa El-Rufai ya shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta hannun lauyoyinsa, yana mai zargin cewa takardar izinin binciken da aka yi amfani da ita wajen shiga gidansa ba ta cika sharuddan doka ba.

A cikin takardar ƙarar, El-Rufai ya ce jami’an ICPC tare da wasu jami’an tsaro sun shiga gidansa da ke yankin Aso Drive a Abuja, inda suka gudanar da bincike tare da kwashe wasu takardu da na’urorin lantarki.

Ya ce, matakin ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, domin yana take masa ‘yancin sirri da mutunci, wanda ya sa yake neman kotu ta ayyana binciken a matsayin haramtacce.

El-Rufai ya kuma buƙaci kotu ta umarci a mayar masa da dukkan kayayyakin da aka ɗauka daga gidansa, tare da biyan shi Naira biliyan 1 a matsayin diyya saboda abin da ya kira cin zarafin haƙƙinsa.

Lamarin na zuwa ne a lokacin da ake cigaba da cece-kuce kan binciken da wasu hukumomin gwamnati ke yi akan wasu lamuran da suka shafi El-Rufa’i.

By Babaji