Kano: APC ta lashe zaɓen cike gurbi yayin da ‘ya’yan mamatan ‘yan majalisa suka yi nasara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar APC ta lashe zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano da aka gudanar a ranar Asabar a mazaɓun Ungogo da Kano Municipal.

Ɗan takarar APC a mazaɓar Kano Municipal, Aliyu Nabil Daneji, ya samu ƙuri’u 7,484 inda ya lashe kujerar, kuma zai wakilci mazaɓar a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Baturen zaɓe, Farfesa Ibrahim Tajo Siraj, ne ya sanar da sakamakon tare da ayyana Daneji a matsayin wanda ya yi nasara.

Haka ma a mazaɓar Ungogo, dan takarar APC, Aminu Sa’ad Sa’ad, ya samu kuri’u 8,975 inda ya lashe kujerar.

Baturen zaɓen mazaɓar, Farfesa Ali Tijjani Abdullahi, ya ayyana Sa’ad a matsayin wanda ya yi nasara tare da ba shi takardar shaidar cin zaɓe.

Rahotanni sun nuna cewa manyan jam’iyyun adawa da suka haɗa da NNPP da PDP da kuma ADC ba su shiga cikin takarar ba.

Sai dai an samu ƙarancin fitowar masu kaɗa kuri’a a yayin zaɓen.

By Babaji