
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Abuja Nyesom Wike, ya amince da soke takardun filaye guda 485 a Abuja sakamakon rashin bin hanyoyi da doka ta tanada na tantance su daga hukumomin gwamnati.
An soke takardun ne bayan nazari akansu da sashen kula da lamuran filaye da haɗin-gwiwar ofishin tsare-tsaren filayen Abuja suka gudanar.
A cewar jami’ai, an gano cewa takardun ba a tabbatar da su akan abin da ya shafi tantancewa ba, lamarin da ya sa da dama aka tabbatar da su a matsayin ‘yan jabu.
Tuni dai a wata takardar sanarwar al’umma aka tabbatar da cire waɗanda aka tabbatar na jabu ne daga sahun masu neman a tabbatar da su a hukumance, musamman waɗanda suka miƙa buƙatarsu daga takardun ƙananan hukumomi domin tantancewa.
Sokewar ta shafi yankuna kamar haka; Ushafa Village Expansion Scheme, Ushafa Extension da kuma Dawaki Extension 1 a Ƙaramar Hukumar Bwari .
Sai kuma Ƙaramar Hukumar Birni (AMAC), inda ya shafi yankunan Kurudu-Jikwoyi Relocation, Kurudu Commercial, Karu Village Extension, Nyanya Phase IV Extension, Jikwoyi Residential, Sabon Lugbe da kuma Lugbe I Extension.
Haka ma Kuchiyako One layout a Ƙaramar Hukumar Kuje, inda nan ma dokar ta shafi cocin Redeemed da Ma’aikatar Shari’a da kuma Staff Multi-purpose Cooperative Society da dai sauransu.
