Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.
Shekara ɗaya bayan rasuwar gogaggen ɗan jarida Lawal Sa’idu Funtua mai aiki da kafar yaɗa labarai na Peoples Daily abokan an aikin sa na cigaba da rasuwar sa.
Lawal Sa’idu ya rasu ne bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya inda akai jana’izar sa a Funtua.
Shugaban ‘yan jarida sashin kafofin yaɗa labarai (Correspondants chapel) Yusuf Ibrahim Jargaba ya zanta da jaridar Manhaja Hausa ya bayyana rasuwar Lawal Sa’idu a matsayin babban rashi ba wai ga ‘yan jaridar jihar Katsina ba har da al’ummar jihar Katsina baki ɗaya.
Ya ce marigayi Lawal Sa’idu mutum mai sauƙin kai wanda baya ƙyamar kowa kuma kowa yasan shi da ƙwarewa wajen rubuce rubuce kan abubbuwan da suka shafi cigaban al’umma musamman abin da ya shafi talaka.
Shima malam Ɗanjuma Katsina mallaki na jaridar Katsina Times kuma wakilan jaridar Almizan wanda babban aminin marigayi ne ya ce za a daɗe ana tunawa da shi musamman a tsakanin abokan aikin sa da makamantan sa.
“Marigayi Lawal Sa’idu ƙwararren ɗan jarida da ya daɗe yana na taimakawa al’ummar jihar Katsina ta hanyar tunatar wa da tsokaci ga gwamnati kan yin abinda ya dace ba tare da tsoro Ba””Inji Ɗanjuma.
Ya ƙara da cewa a duk lokacin da marigayi yayi rubutu a jaridar sa,sai jihar ta motsa domin tsage gaskiya ko bata yiwa hukumomi daɗi ba.
Kwamred Mannir Suleiman ɗan uwa ne kuma abokin marigayi Lawal Sa’idu,ya bayyana cewa ya daɗe bai ji mutuwar da ta girgiza shi ba irin wannan domin yadda suka shaƙu da marigayi.
“Mutum ne mai sauƙin kai kuma bashi da kwaramniya ga shi da barkwanci,”Inji kwamred Suleiman.
Marigayi Lawal Sa’idu ya fara aiki a gidan rediyon jihar Katsina kafin daga baya ya koma jaridar Democrate daga nan ya wuce zuwa gidan rediyo da talabijin na DITV Kaduna.
Ya kuma yi aiki a jaridar Today daga baya Jaridar Leadership a matsayin wakilin ta a Katsina kafin ya koma Jaridar peoples Daily.
Ya rasu ya bar matan sa biyu da ya’ya da dama.
