
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya tsige Kayode Egbetokun daga muƙaminsa na sufeto janar na rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
A cewar jaridar ShaharaReporters, an yi zargin Tinubu ya fitar da umarnin cire Egbetokun ne tun a jiya Litinin.
Haka kuma, takardar umarnin ta bayyana cewa Tunji Disu, wanda Mataimakin Sufeto Janar ne da ke sanya ido a sashen binciken manyan laifuka (FCID) a Alagbon, Jihar Legas, ne zai maye gurbin Egbetokun.
Wasu manyan jami’an rundunar da majiyoyi daga Hukumar kula da lamuran ‘Yan sanda sun tabbatar da al’amarin ga jaridar ShaharaReporters a yau Talata.
Wata daga cikin majiyoyin ta ce, Egbetokun ya je Fadar Shugaban Ƙasa a jiya inda aka umarce shi ya je ya shirya takardarsa ta miƙa ragamar jagorancin rundunar ga wani.
Majiyar ta ƙara da cewa, “Bai da ƙwarewa. Yana kwaɗayin mulki. Shugaban ƙasar ya ce ya fice domin mayar da hankali akan yi wa kansa magani. Kun san yana da matsalar da ta shafi cutar ƙoda.”
ShaharaReporters ta ruwaito cewa, wasu jami’an ‘yan sanda tuni suka fara bayyana farin cikinsu a game da matakin.
Riƙe muƙamin da Egbetokun ya haddasa cece-kuce acikin jama’a da ƙungiyoyin al’umma musamman bisa la’akari da yadda jami’an hukumar ke ji da lamuran masu zanga-zanga, ƙarin zangon shekarun murabus na 60 or 35 na aiki da kuma cigaba da take dokokin rundunar.
