Masu azancin magana kan ce “zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki.” Haƙiƙa, duk wani ci gaba da gwamnati ko masu hannu da shuni ko kuma ɗaidaikun mutane za su samar ba zai ɗore ba muddin babu zaman lafiya. Wannan ne ya sa duk wani ɗan ƙasa nagari ba ya da wata fata a ƙasarsa face samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A ƙoƙarin samar da wannan zaman lafiya, gwamnati ta kafa hukumomi daban-daban kamar ’yan sanda, sojoji, jami’an tsaro na farin kaya (DSS), Ciɓil Defence da sauransu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Haka kuma, gwamnati ta kafa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi (NDLEA) wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen tsarkake al’umma daga illar shaye-shayen ƙwayoyi.
A ƙarƙashin jagorancin Janar Buba Marwa mai ritaya da sauran shugabannin hukumar a fadin jihohi, NDLEA ta samu nasarori masu yawa. Waɗannan nasarori ne har wasu ke zargin cewa hukumar na yin “wankin ido” ko wani irin tsafi wajen gano masu safara da amfani da miyagun kwayoyi. Amma wannan zargi ba shi da tushe. Nasarorin da hukumar ke samu sun samo asali ne daga ingantaccen horo da jajircewar jami’anta.
A ganina, kusan duk masu aikata laifuka da ta’addanci za ka taras suna amfani da miyagun kwayoyi domin kawar da hankalinsu kafin su aikata laifuka. Idan za a wayi gari a ƙasar nan babu masu safara ko amfani da miyagun kwayoyi, to za a sami raguwar laifuka sosai, har ma a zagaye kasa ba a samu masu aikata ta’addanci ba.
Saboda haka, idan jama’a suka bai wa hukumar NDLEA cikakken goyon baya da haɗin kai, za ta samu damar kawar da masu safara da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi. Wannan kuma zai samar da al’umma mai nagarta. Idan hakan ta faru, sauran hukumomin tsaro kamar ’yan sanda da sojoji za su samu saukin aiki, domin adadin masu aikata laifuka zai ragu matuka.
Ya kamata mu lura cewa mafi yawan masu shaye-shayen miyagun kwayoyi matasa ne. Matasan nan su ne iyayen gobe da shugabannin ƙasa na gaba. Idan zukatansu suka lalace, hakan zai haifar da karuwar yara marasa tarbiyya da al’umma marar nagarta. Shaye-shaye na jefa mutane cikin sata, garkuwa da mutane, fashi da makami, kisan kai, daba, kalare, sara-suka da sauran munanan laifuka.
Saboda haka, a fahimtata, NDLEA hukuma ce tilo da za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya ta hanyar kawar da masu safara da masu amfani da miyagun ƙwayoyi. Wannan kuwa shi ne muradin kowane dan kasa nagari.
Ina kira da babbar murya ga jama’a a ko ina suke da su bai wa hukumar NDLEA cikakken goyon baya da haɗin kai. Domin an ce hannu daya ba ya daukar jinka, kuma hannu da yawa maganin ƙazamar miya. Idan muka hada kai da gwamnati, za mu iya gina al’umma mai tarbiyya da zaman lafiya.
Daga HARUNA MUHAMMAD KATSINA 07039205659. 08121355933.
