
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani ɗan jarida a Jihar Kano mai suna Abdul baƙi Ali Ahmed Sharifai ya nuna aniyarsa ta ɗaukar matakin shari’a akan wani zargin cin zarafi da ya ce wani jami’in gwamnatin jihar ya yi masa a yayin wani taron al’umma.
Al’amarin ya faru ne a filin Race Course da ke cikin birnin Kano, lokacin gudanar da Argungu Motor Rally, wani bangare na bukukuwan bikin Argungu International Fishing and Cultural Festival karo na 61.
An ruwaito cewa, jami’in gwamnatin da ake zargi, Auwal Sani Rogo, wanda ke aiki a matsayin Babban Mai Rahoto na Musamman da gwamnatin Kano, ya yi musayar yawu da ɗan jaridar ne jim-kaɗan bayan kammala wata hira da wasu ‘yan jarida suka gudanar a wajen taron.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a gaban manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, da Kwamishinar Al’adu da Yawon Bude Ido, Hajiya Aisha Lawan Saji Rano, da kuma Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano, Alhaji Abba El-Mustapha.
Bayan haka ne ɗan jaridar ya garzaya ofishin ‘yan sanda na Bompai, wato Hedikwatar rundunar ‘yan sandan Kano, inda ya shigar da ƙorafi a hukumance.
Sai dai rahotanni sun ce jami’in da ake zargi bai amsa gayyatar ‘yan sanda ba, lamarin da wasu majiyoyi suka ce yana fakewa da ofishin gwamnatin jihar domin kaucewa kama shi.
Daga bisani, Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Waiya, ya gayyaci ɗan jaridar domin sasanci tare da ba shi tabbacin cewa zai shiga tsakani domin ganin an warware matsalar cikin lumana.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance ko neman afuwa da aka fitar daga jami’in gwamnatin, gwamnatin ko ofishin masu ba Gwamna Abba Kabir Yusuf Shawara na musamman.
Majiyoyi na kusa da ɗan jaridar sun bayyana cewa yana ganin ɗaukar matakin shari’a shi ne zabin da ya rage masa domin kare hakkinsa da martabar aikinsa musamman bisa la’akari da cewa yana gudanar da aikinsa ne bisa tsari a lokacin faruwar al’amarin.
Wannan al’amarin ya haifar da cece-kuce acikin ‘yan jarida da masu ruwa da tsaki akan muhimmancin mutunta aikin jarida da kuma yadda ya kamata jami’an gwamnati su mu’amalanci kafafen yada labarai a tarukan da suka shafi jama’a.
