Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Ƙungiyar sada zumunta ta Gidan Alheri, reshen Dangin Juna Afirka Initiative (DJAI), ta raba kayan abinci da tallafin kuɗi ga mambobinta da sauran mabuƙata a Jihar Gombe domin sauƙaƙa raɗaɗin rayuwa a watan Ramadan.
Tallafin ya ƙunshi gero, sukari, buhunan shinkafa masu nauyin kilo 10, taliya (spaghetti) da kuma kuɗi naira 5000 ga kowanne daga cikin waɗanda suka amfana.
Mai taimaka wa Gwamnan Jihar Gombe kan harkokin tsaro da hulɗa da jama’a, Yusuf Musa Danbayo, ya bayar da tallafin gero da sukari ga mambobi 20, yana mai cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan jin ƙai da tallafa wa marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Shugaban ƙungiyar, Sagir A.A. Haruna, wanda shi ma ya tallafa da shinkafa da kuɗi, ya ce rabon tallafin azumi ya zama al’ada a duk shekara.
Ya bayyana cewa bana ita ce shekara ta huɗu a jere da ƙungiyar ke shirya irin wannan shiri.
Ya ƙara da cewa an kafa kwamitin musamman da ke kula da shirin ciyar da mabuƙata da tsangayun almajirai, inda ake haɗa abinci kamar kunu, ƙosai da taliya a kowace rana na tsawon kwanaki 25.
Haka kuma, ya ce a ƙarƙashin uwar ƙungiyar ta ƙasa, ana zaɓar jiha guda a duk shekara domin gudanar da babban shirin tallafa wa gajiyayyu.
Wasu daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin sun nuna farin ciki tare da yabawa shugabannin ƙungiyar bisa ƙoƙarin su na kula da walwalar mambobi da sauran mabuƙata.
Baya ga haka, ƙungiyar ta kuma miƙa tallafin kuɗi da sutura ga ɗaya daga cikin mambobinta, Aisha, bayan gobarar da ta ƙone shagon sana’arta.
