Cin zarafin ɗan jarida: SSR na Gwamnan Kano ya nemi afuwar ‘yan jarida

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano tare da SSR na Gwamna Abdullahi Rogo sun bai wa ƴan jarida hakuri kan zargin cin mutuncin ɗaya daga cikin mambobinsu, bayan wani zaman sulhu da aka gudanar domin warware rikicin.

Sulhun ya biyo bayan zaman da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kira a ranar Laraba domin daidaita al’amuran da suka lalace tsakanin ɓangarorin.

Taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyar Kano Online Media Chapel ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Kwamared Abubakar Abdulƙadir Dangambo, da daraktocin ma’aikatar yaɗa labarai, tare da ɗan jarida kuma tsohon shugaban ƙungiyar ƴan jaridu ta ƙasa, Comrade Abdullahi Datti Arzai.

Da yake jawabi yayin taron, kwamishina Waiya ya buƙaci SSR Rogo da sauran jami’an gwamnati da su riƙa kyautata alaƙa da ’yan jarida domin ci gaban jihar. Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da kafafen yaɗa labarai, yana mai amincewa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen wayar da kan al’umma kan manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

Shi ma a nasa ɓangaren, Shugaban Kano Online Media Chapel, Comrade Abdulƙadir Dangambo, ya gode wa kwamishinan bisa saurin shiga tsakani da ya yi wajen warware matsalar. Sai dai ya nuna cewa ba wannan ne karo na farko da ake zargin SSR Rogo da irin wannan hali ba, lamarin da ya bayyana a matsayin abin takaici.

Kazalika, ya kuma ja hankalin jami’an gwamnati da su fahimci muhimmiyar rawar da ƴan jarida ke takawa a cikin al’umma da kuma tasirin aikinsu wajen inganta dimokuraɗiyya da gaskiya.

Lamarin dai ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na cikin da wajen ƙasar nan suka yi Allah wadai da faruwar al’amarin, tare da bai wa gwamnatin jihar wa’adin sa’o’i 24 ta ɗauki mataki ko kuma su ɗauki matakin shari’a.

Ɓangarorin sun bayyana fatan cewa sulhun da aka cimma zai taimaka wajen gyara alaƙa da kuma kauce wa maimaita irin wannan lamari a nan gaba.

By ukarofi