Gwamnatin Kano ta ƙaryata rahoton Amnesty International

Spread the love

Daga RABIU SANUSI

Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da zarge-zargen da Amnesty International ta gabatar, inda ta bayyana su a matsayin marasa tushe masu yaudara da kuma kauce wa gaskiya.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, gwamnatin ta mayar da martani ga rahoton mai taken “Kano: Escalating Repression Endangers Freedom of Expression,” wanda ya zargi gwamnatin da amfani da jami’an tsaro wajen kama ko takura wa masu sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin Kano na da cikakken ƙuduri wajen kare haƙƙin ɗan Adam ciki har da ‘yancin fadin albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.

Gwamnatin ta bayyana cewa ba ta taɓa umartar wata hukumar tsaro da ta riƙa takura ko tsoratar da kowa saboda ra’ayinsa ba, tana mai jaddada cewa duk da kasancewar ‘yancin faɗin albarkacin baki haƙƙi ne na doka ba ya bai wa kowa damar yin ɓatanci, yaɗa ƙarya tayar da hankali ko kuma cin mutuncin wasu.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa jami’an tsaro ciki har da Department of State Services na gudanar da ayyukansu ne bisa ƙa’idojin doka kuma duk wani kama ko gayyata na faruwa ne sakamakon ƙorafe-ƙorafe ko zargin aikata laifuka kamar cin zarafi ta yanar gizo, ɓata suna ko tayar da fitina.

A cewar gwamnatin, ba ta da ikon sarrafa ayyukan hukumomin tsaro na tarayya, amma tana goyon bayan duk matakan da ake ɗauka na daƙile laifukan yanar gizo da kuma kare mutunci da zaman lafiya a cikin al’umma.

Sanarwar ta nuna damuwa kan yadda wasu ke amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa bayanan ƙarya da kai hare-hare na ƙashin kai a sunan sukar gwamnati.

Gwamnatin ta kuma jaddada cewa ta samar da yanayi mai kyau ga kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula ta hanyar shirin Open Government Partnership da ke bai wa al’umma damar shiga harkokin mulki.

Ta ƙara da cewa jama’a na da ‘yancin bayyana ra’ayoyinsu kan tafiyar da gwamnati ba tare da tsangwama ba, tare da jaddada cewa sukar gwamnati mai ma’ana na da muhimmanci ga ci gaban dimokuraɗiyya.

Sai dai gwamnatin ta nuna cewa akwai bambanci tsakanin suka da ɓatanci, haka kuma tsakanin adawa da tayar da zaune tsaye.

A ƙarshe, gwamnatin Kano ta jaddada cewa ba ta tsananta wa masu amfani da kafafen sada zumunta ko ‘yan adawa, tana mai cewa duk wani mataki da jami’an tsaro ke ɗauka yana ƙarƙashin dokokin da suka shafi laifukan yanar gizo da kuma kare haƙƙokin jama’a.

Ta kuma buƙaci ƙungiyoyi da masu sharhi su tabbatar da gaskiyar bayanai kafin yanke hukunci da ka iya haifar da ruɗani ko tada hankali.

Gwamnatin Kano ta tabbatar da ƙudurinta na ci gaba da bin tafarkin dimokuraɗiyya, doka da oda, tare da tabbatar da cewa ana amfani da haƙƙin ɗan Adam cikin gaskiya da alhaki.

By ukarofi