Gwamnatin Kano ta sanar da ranar hutun Azumin Ramadan da ƙaramar Sallah

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranar fara hutun Azumin Ramadan da na ƙaramar sallah ga dukkanin makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa, kamar yadda yake ƙunshe a cikin jadawalin shekarar karatu ta 2025/2026 da aka amince da shi, za a fara hutun ne a ranar Asabar 1 ga Maris, 2026, ga dukkan ɗalibai masu kwana a makaranta da na rana.

An kuma buƙaci iyaye da masu kula da ɗaliban da ke makarantun kwana da su je su ɗauki ‘ya’yansu tun da safiyar Juma’a 30 ga Fabrairu, 2026.

Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaliban makarantun kwana za su koma makaranta ranar Lahadi 22 ga Maris, 2026, yayin da ɗaliban rana za su koma ranar Litinin 23 ga Maris, 2026.

An bayyana cewa zangon karatu na biyu zai ci gaba daga ranar Lahadi 22 ga Maris, 2026, kuma zai ƙare ranar Asabar 18 ga Afrilu, 2026.

Gwamnatin ta umarci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su bi wannan umarni, tare da gargaɗin cewa duk wata makaranta da ta saɓawa wannan tsari za a ɗauki mataki a kanta.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda, ya yi kira ga iyaye da masu kula da ɗalibai da su tabbatar da bin ranakun komawa makaranta kamar yadda aka tsara.

Ya kuma gode wa iyaye da al’ummar jihar bisa haɗin kai da goyon bayan da suke bai wa Ma’aikatar Ilimi tare da yi wa ɗalibai fatan kammala azumin Ramadan cikin nasara da gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali.

By ukarofi