Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ta kai Dala biliyan 50.45 a ranar 16 ga Fabrairu, 2026 ita ce mafi girman mataki da aka samu cikin shekaru 13 da suka gabata.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron kwamitin manufofin kuɗi (MPC) karo na 304 a Abuja.
Cardoso ya bayyana cewa, hauhawar ajiyar kuɗaɗen na nuna ƙaruwar ingancin yanayin tattalin arziki da kuma ƙarin amincewar kasuwanni ga alƙiblar manufofin kuɗin ƙasa.
A cewarsa, ajiyar na ba da damar biyan buƙatun shigo da kaya da ayyuka na tsawon watanni 9.68, alamar da ke nuna ƙarfi da ɗorewar kuɗin waje.
Ya danganta wannan nasara da kyawawan sauye-sauyen cinikayya, ribar da aka samu a asusun hada-hadar waje (current account surplus), da kuma bunƙasar fitar da kayayyakin da ba na mai ba.
“Ajiyar kuɗaɗen waje ita ce mafi girma da muka samu cikin shekaru 13. Mun ga kyawawan alamomi dangane da yadda tattalin arziki ke farfazowa. Cinikayya ta inganta, asusun hada-hadar waje na cikin ƙoshin lafiya, sannan fitar da kayayyakin da ba na mai ba ta ƙaru,” inji shi.
Gwamnan ya jaddada cewa amincewar kasuwa ita ce ginshiƙin wannan ci gaba. Ya ce CBN ya shiga tarurrukan ƙasa da ƙasa domin bayyana manufofinsa, ya yi alƙawurra, tare da tsayawa kan waɗannan alƙawurra cikin gaskiya da bayyana gaskiya.
“Ba tare da amincewar kasuwa ba, duk wata dabara da za a aiwatar ba za ta kai ga sakamako mai gamsarwa ba,” inji Cardoso, yana mai cewa buɗe ƙofofi da tsabta a tafiyar manufofi sun taimaka wajen farfaɗo da kwarin gwiwar masu zuba jari.
Sai dai duk da wannan ci gaba, Cardoso ya yi gargaɗin cewa akwai barazana daga cikin gida da waje da ka iya kawo tangarɗa. Ya ambaci yiwuwar girgizar tattalin arzikin duniya, sauyin farashin mai, da kuma matsin lambar kashe kuɗaɗe kafin zaɓe a matsayin abubuwan da ya kamata a kula da su.
“Ba wanda ke da madubin hangen gaba. Farashin mai da yadda zai sauya abu ne da ake iya hasashe kawai. Haka kuma, kashe kuɗade ba tare da tsari ba kafin zaɓe na iya lalata kwanciyar hankali da muka samu,” inji shi.
CBN ya yi hasashen cewa ajiyar kuɗaɗen na iya kaiwa kusan dala biliyan 51 kafin ƙarshen 2026. Idan hakan ta tabbata, zai zama mafi ƙarfi tun watan Mayun 2013, lokacin da ajiyar ta kai kusan dala biliyan 48.51.
A ƙarshen 2025, ajiyar ta tsaya a kusan dala biliyan 45.5, daga biliyan 40.8 a farkon shekarar, alamar da ke nuna cewa tafiyar ta hau kan turbar daidaito da haɓaka a farkon 2026.
A ƙarshe, masana na ganin cewa ci gaba da tsayawa kan manufofi masu dorewa, kauce wa sauya matsayi ba tare da shiri ba, da kuma ƙarfafa hadin gwiwa da ɓangaren masu zuba jari, su ne mabuɗan ɗorewar wannan nasara.
