Abin da ya biyo bayan sa hannu kan dokar zaɓe ta 2026

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan Dokar Gyaran Zaɓe ta 2026 a Fadar Shugaban ƙasa, ba kawai ya kammala wata takarda ta doka ba ne, a’a ya rufe babi na watanni masu cike da muhawara, saɓani, zanga-zanga da siyasar gwagwarmaya tsakanin majalisun dokoki da masu ruwa da tsaki ne.

Ga ’yan Nijeriya da dama, wannan mataki ya zarce bikin sanya hannu. Wani muhimmin al’amari ne da zai iya zayyana sahihancin babban zaɓen 2027.

A wajen bikin sanya hannun, wanda ya samu halartar Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai Abbas Tajudeen da sauran manyan jami’an gwamnati, an mayar da ƙudirin mai kusan sashe 155 ya zama doka. Amma tafiyar da ta kai ga wannan rana ba ta kasance mai sauƙi ba.

Daga cikin sassan dokar, Sashe na 60 shi ne ya fi tayar da ƙura. Tun da farko, Majalisar Wakilai ta amince da wajabcin tura sakamakon zaɓe ta hanyar lantarki kai tsaye daga rumfunan zaɓe zuwa dandalin kallon sakamako na Hukumar Zaɓe.

Sai dai Majalisar Dattawa ta yi fatali da wajabcin, ta bar batun tura sakamako ta hanyar lantarki a matsayin zaɓin da za a iya yi, ba tilas ba, kamar yadda aka tanada a dokar 2022.

Bayan zanga-zanga da matsin lamba daga jama’a, Majalisar Dattawa ta sake zama tare da kaɗa ƙuri’a ta raba gardama. Daga bisani, Shugaban Majalisar Dattawa ya tabbatar da cewa tsarin a “zaɓi” zai tsaya.

Majalisar Wakilai, wadda tun farko ta goyi bayan wajabcin, daga bisani ta sauya matsayarta ta rungumi tsarin Majalisar Dattawa.

A tsakiyar wannan sulhu akwai takardar EC8A, wadda jami’in rumfar zaɓe ke cike wa nan take bayan ƙirga ƙuri’u. A kotunan sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe, wannan takarda ce ake dogaro da ita a matsayin hujjar farko ta sakamakon da aka samu a asali.

Sabuwar dokar ta bar damar tura sakamako ta lantarki, amma idan an samu matsalar intanet, EC8A ce za ta zama tushen tattarawa.

Masu goyon bayan gyaran na ganin hakan sassauci ne mai ma’ana a ƙasa mai fama da tangarɗar sadarwa. Masu suka kuwa na kallon hakan a matsayin barin wata ƙofa a buɗe a mafi muhimmancin matakin zaɓe.

Shugaba Tinubu ya kare matakin da cewa dole ne a yi la’akari da haƙiƙanin yanayin fasaha a ƙasar. Ya nuna cewa ƙuri’a da ƙirga su har yanzu ana yin su ne da hannu, kuma lissafin da ke cikin EC8A shi ne ginshiƙin sahihanci.

Ya kuma yi gargaɗin yiwuwar tangarɗa, katsalandan ko kutse ta yanar gizo, yana mai cewa barin tsarin a matsayin zaɓi zai iya kauce wa matsalolin da za su tayar da ƙura fiye da warware ta.

ƙungiyoyi kamar Yiaga Africa, The Kukah Centre da TAF Africa sun bayyana takaicinsu, suna cewa an rasa wata dama ta yin gyara mai zurfi. Sun kuma soki kuɗin rajistar sabuwar jam’iyya na naira miliyan 50 a matsayin abin da zai iya takura shiga siyasa.

A arewacin ƙasar, ƙunguyar Tuntuɓƙ ta Arewa ta ce sanya hannun ya zama dole saboda ƙarancin lokaci kafin 2027, amma ta nemi cikakken bayyana dokar ga jama’a. A kudu maso yamma kuma, Afenifere ta soki kin wajabta tura sakamako kai tsaye, tana cewa hakan ka iya cutar da sahihancin dimokuraɗiyya.

Baya ga Sashe na 60, an gyara Sashe na 28(1), inda aka rage lokacin da INEC za ta fitar da sanarwar zaɓe daga kwanaki 360 zuwa kwanaki 300 kafin ranar zaɓe, domin bai wa hukumar sassauci wajen tsara jadawali.

Tsohon Kwamishinan INEC, Festus Okoye, ya gargaɗi cewa jinkirin fayyace doka kan iya haifar da ruɗani kamar yadda aka gani kafin zaɓen 2023.

A zahiri, damuwar ’yan Nijeriya ta sauya daga yadda ake kaɗa ƙuri’a zuwa abin da ke faruwa bayan an bar rumfa. Fasahohi kamar BɓAS sun rage rikice-rikice a matakin tantance masu zaɓe. Amma tafiyar sakamako daga rumfa zuwa cibiyar tattarawa ita ce har yanzu wuri mai zafi.

Masu suka na ganin barin tura sakamako a matsayin zaɓi alama ce ta fifita sassauci a kan wajabci. Masu goyon baya kuma na cewa sassauci ya dace a ƙasa mai faɗi da matsalolin sadarwa.

Yanzu da dokar ta zama doka, aiwatarwa ce za ta zama gwajin gaskiya. Domin a ƙarshe, zaɓe ba a auna shi da kyawun rubutun doka ba, sai da amincewar jama’a da sakamakon da aka bayyana.

Yayin da Nijeriya ke tunkarar 2027, ainihin gwajin Dokar Zaɓe ta 2026 ba Sashe na 60 kaɗai ba ne. Gwajin shi ne ko ɗan ƙasa zai yarda cewa tafiyar da ƙuri’arsa daga takardar zaɓe zuwa sanarwar ƙarshe tafiya ce mai tsaro, gaskiya da sahihanci.

Ita doka ana iya gyara ta. Amma amana idan ta zube, dawo da ita ya fi wahala.

By ukarofi