El-Rufa’i ya nemi kotu ta haramta wa ICPC, EFCC da SSS rufe asusun bankunansa da ƙwace kadarorinsa

Spread the love

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta neman a hana hukumomin ICPC, EFCC, DSS da kuma Antoni Janar na Ƙasa (AGF) ɗaukar matakin rufe masa asusunsa na banki ko ƙwace kadarorinsa.

A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/368/2026 da lauyansa Oluwole Iyamu (SAN) ya shigar, El-Rufai ya nemi kotu ta bada umarnin wucin-gadi domin hana su aiwatar da komai har sai an kammala sauraron shari’arsa.

Ya kuma buƙaci kotun da ta tabbatar da cewa kuɗin fansho da alawus-alawus din barin aiki da ya karɓa bayan kammala wa’adinsa daga 2015 zuwa 2023 halalliyarsa ne ba waɗanda aka samu ta haramtattun hanyoyi ba.

Sannan, ya nemi kotu ta bayyana cewa duk wani yunƙuri na neman izinin ƙwace ko rufe asusunsa ko kadarorinsa ba tare da hujja mai ƙarfi ba zai saɓa wa kundin tsarin mulki, musamman sashe na 36(5).

Kazalika, ya nemi a hana hukumomin daukar duk wani mataki kan asusunsa na bankunan Zenith, GT da kuma Access.

Har ila yau, tsohon gwamnan ya buƙaci kotu ta sa su biya shi diyyar Naira biliyan 1 saboda barazanar take haƙƙinsa da kuma Naira miliyan 100 a matsayin kudin shari’a.

A cewarsa, ba a taɓa samun sa da wani laifi ba a duk muƙaman da ya riƙe a baya, kuma a shirye yake ya ba da haɗin kai ga duk wani bincike bisa ƙa’ida da aka shirya gudanarwa akansa.

By Babaji