Kano: Hukumar Yaƙi da Rashawa ta tilasta wa ɗan Kwankwaso da wasu tsoffin kwamishinoni dawo da motocin gwamnati

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Al’umma da Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano ta ƙwato motoci biyar na gwamnati daga hannun wasu tsofaffin kwamishinoni da suka yi murabus daga majalisar zartarwar jihar.

Shugaban hukumar, Sa’idu Yahaya, ya ce an ɗauki matakin ne bayan sun ƙi mayar da kadarorin gwamnati duk da gargadi da aka yi musu, inda aka samu umarnin kotu kafin aiwatar da aikin.

Ya bayyana cewa biyu daga cikin motocin su ne ainihin waɗanda gwamnati ta saya, yayin da bincike ya nuna an sayar da sauran, aka maye gurbinsu da wasu motoci.

Hukumar ta musanta zargin siyasa akan al’amarin, tana mai cewa matakin ya dace da doka domin kare dukiyar al’ummar Kano.

Wani tsohon babban ma’aikacin gwamnati, Mohammad Tukur, ya ce babu wata doka da ta bai wa kwamishina damar riƙe motar gwamnati bayan barin aiki, face gwamna ya ba da izini na musamman.

Daga cikin waɗanda aka ƙwato motocin hannunsu akwai tsohon Kwamishinan Tsaro, Air Vice Marshal Ibrahim Umar, tsohon Kwamishinan Matasa, Mustapha Rabiu Kwankwaso, tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dr Yusuf Ibrahim Kofar Mata, tsohon Kwamishinan Jin Kai, Dr. Adamu Aliyu Kibiya, da tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo. Hukumar ta kuma ce za ta cigaba da ɗaukar matakan da suka dace domin bai wa dukiyar gwamnatin kariya.

By Babaji