
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Ƙolin Shari’a a Nijeriya (SCSN) ta ce babu wani iko ko ƙarfin mulki da zai hana Musulmi aiki da Shari’ah a ƙasar.
Sakataren Majalisar, Nafi’u Baba Ahmad ya bayyana haka a wata takarda yayin da yake tsokaci game da rahoton da kwamitin majalisar dokokin Amurka ya miƙa wa Shugaba Donald Trump a kwanan nan.
Hakan na zuwa ne bayan da mambobin kwamitin, wato Ɗan majalisa Riley Moore da Chris Smith suka kammala bincike akan zargin kisa kiyashi ga al’ummar Kirista a Nijeriya.
A rahoton nasu, sun bayyana dokokin shari’a da ɓatanci a matsayin manyan ababen da ake da matsala akansu.
Daga shawarwarin da suka bayar akwai neman a soke hukunce-hukuncen dokokin Shari’ah da ɓatanci tare da amfani da yarjejeniyar tsaro ta Amurka da Nijeriya da kuma hukunci ga waɗanda suak saɓa mata ko haramta musu biza.
A cewar ‘yan majalisar, dokokin ɓatanci da ake amfani da su a Arewacin Nijeriya na tauye ‘yancin bayyana ra’ayi da ke harin al’ummar Kirista da tabbatar da laifi akansuba tare da bin hanyoyin da doka ta amince da su ba.
To saidai SCSN ta ce rahoton Amurkawan ya yi kuskuren ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake yi wa Kiristoci “kisan kiyashi” da kuma tauye haƙƙin al’ummar Musulmin Nijeriya aiki da hukunce-hukuncen Shari’ah.
A cewarta, “domin warwarewa, Shari’a ta ƙunshi tsarin rayuwa ga Musulmai, da ya haɗa da imani da ɓoyayyun abubuwa, gudanar da kai bisa tsari, zamantakewa da halastattun hukunce-hukunce.”
Ta ƙara da cewa, addinin shi ne bin hanyar Mahalicci waɗanda ya tsara wa Musulmi wajen gudanar harkokinsu da na zamantakewa acikin al’umma.
Kazalika, sanarwar ta bayyana cewa aiki da Shari’ah a Nijeriya ya samu sahalewar dokar ƙasa, wadda ta bayar da ‘yancin addini da biyayya ga dokokinsa yadda ya tsara.
