
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata kotun gunduma da ke Amurka, ta yanke wa tsohon babban jami’i a Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), Paulinus Okoronkwo hukuncin ɗaurin watanni 87 a gidan yarin tarayya bisa samun sa da hannun a laifin karɓar cin hancin Dala miliyan 2.1 da aka danganta da wani kamfanin mai na ƙasa-da-ƙasa.
Okoronkwo, wanda a baya shi ne janar manaja na sashen samar da albarkatun mai na NNPC, an same shi ne da laifuka da dama da suka haɗa da sauya akalar kuɗaɗen ƙasa, ƙaurace wa biyan haraji da gangan da kuma ƙoƙarin hana a yi adalci.
Mai Shari’a John Walter na kotun ne ya gabatar da hukuncin, sannan ya kuma umarci tsohon jami’in da ya biya jimillar Dala 923,824 ga Hukumar Tattara Haraji ta ƙasa (IRS) a matsayin ƙwato haƙƙinta.
Ƙari akan zuwa gidan yarin, kotun ta umarci a ƙwato Dala miliyan 1.04 na kuɗaɗen da aka sayar da wata kadara da aka alaƙanta mallakar da kuɗaɗen na haram.
A cewar lauyoyin da suka gabatar da shari’ar biyan cin hancin ya samo asali ne daga kamfanin Addax Petroleum na ƙasar Switzerland, wanda reshe ne na Sinopec da ke ƙasar Chana.
Masu bincike sun shaida wa kotun cewa Dala miliyan 2.1 da aka tura wa asusun kamfanin shari’a na Okoronkwo a shekarar 2015, an fake da su ne a matsayin na neman shawarwarin shari’a.
An samu Okoronkwo da laifin ne tun a watan Agustan 2025 bayan wata shari’a da aka yi a jihar Kalifoniya, wanda ya kawo ƙarshen binciken tsawon lokaci akan rashawa na ƙasa-da-ƙasa da ya ƙunshi kwangilolin fannin makamashi.
