An fitar da jaddawalin ‘yan 16 na Kofin Zakarun Turai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da aka kammala zagayen wasannin cike gurbi a gasar zakaran nahiyar Turai, wato UEFA Champions League na 2025/2026, Hukumar UEFA ta shirya ƙungiyoyin da za su kara da juna a rukunin ‘yan 16.

Hakan na zuwa ne ƙasa da watanni uku da za a ƙarƙare gasar, wadda ƙungiyar PSG ta lashe a kakar wasan da ta gabata.

Ga jaddawalin yaɗa wasannin suke kamar yadda Blueprint.ng ta ruwaito:

Real Madrid vs Manchester City

Bodø/Glimt vs Sporting

PSG vs Chelsea

Newcastle vs Barcelona

Galatasaray vs Liverpool

Atletico Madrid vs Tottenham

Atalanta vs Bayern Munich

Bayer Leverkusen vs Arsenal

Ga tsarin yadda aka raba ƙungiyoyin zuwa kashi biyu:

By Babaji