
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya umarci a gaggauta dakatar da tsarin biyan kuɗaɗe ta na’ura a filayen jiragen sama na Gwamnatin Tarayya.
Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci-gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo ya sanar da haka a yau Laraba bayan zaman Majalisar Zartarwa (FEC) da aka gudanar da Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja.
Ya ce, Shugaban ƙasar ya kuma umarci a gaggauta dawo da tsarin da zai taimaka wajen inganta tsarin ta yadda al’umma da dama za su amfana.
A ranar 1 ga watan Maris ɗin shekarar nan ta 2026 ne Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama Ta Ƙasa, FAAN, ta sanar da dakatar da karɓar tsabar kuɗi daga hannun masu ababen hawa a shingayen karɓar kuɗin, (Toll Gates) da aka kafa daidai shiga filayen jiragen, sai dai su biya ta hanyar amfani da katin biyan kuɗi ko ta internet.
Saidai wannan al’amari ya riƙa haifar wa fasinjojin jiragen sama tsaiko, inda direbobi su ka riƙa shafe sa’o’i wajen bin layin biyan kuɗin.
Haka kuma, lamarin ya riƙa janyo wa jirage na tashi su na barin fasinjoji, ko kuma fuskantar jinkirin zuwa a ɗauke fasinjojin bayan sun sauka daga jirgi.
Keyamo ya ce shugaba Tinubu ya damu da wahalhalun da ƴan Najeriya ke sha a shingayen karɓar kuɗin, don haka ne ya umarci ma’aikatar ta koma tsarinta na da domin sauƙaƙa musu.
