Kofin duniya na 2026: Super Eagles ta ɗebe tsammani bayan FIFA ta tabbatar da DR Congo a gasar

Spread the love

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) ta ce ƙasar DR Congo ce za ta wakilci Afrika a wasannin cike gurbi domin shiga gasar Kofin Duniya na 2026, yayin da Super Eagles ta Nijeriya rasa damar.

Matakin da ya kawo ƙarshen burin Super Eagles ta Nijeriya na zuwa gasar kai tsaye.

An shirya gasar tantancewar daga ranar 26–31 Maris 2026 a biranen Guadalajara da Monterrey, na ƙasar Mexico, inda ƙungiyoyi shida za su fafata don samun guraben ƙarshe biyu na gasar cin kofin gasar duniya.

Ƙungiyar kwallon kafa ta Nijeriya (NFF) ta gabatar da ƙorafi, tana ikirarin cewa DR Congo ta yi amfani da ‘yan wasa marasa cancanta a wasan CAF da ya ƙare 1–1 kafin a tafi bugun fanareti a watan Nuwamban 2025. Duk da haka, FIFA ba ta yi wata sanarwa ba kan janye DR Congo ko bayar da dama ga Nijeriya ba.

A halin yanzu, Najeriya ba ta cikin jerin ƙungiyoyin da suka tabbata za su shiga gasar cin kofin duniya, yayin da DR Congo za ta wakilci Afirka a gasar tantancewar.

Duk da cewa har yanzu akwai ƙaramin fata na canjin hukunci daga FIFA, rashin jawabi daga hukumar yana sanya samun damar shiga gasar ya zama ƙalubale ga Super Eagles yayin da lokacin gasar ke ƙara matsowa.

By Babaji